1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta dora laifin turmutsutsu akan mahajjata masu taurin kai

January 13, 2006
https://p.dw.com/p/BvCT

Kasar Saudiya ta dora laifin turmutsutsu da akayi jiya wajen jamra da yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla mutane 345,akan mahajjata masu taurin kai da basu san ya kamata ba,amma sauran musulmi kuma sun ce rashin samarda kyakkyawar tsaro,ya janyo hadarin na jiya.

Sai dai kuma alkalin alkalai na Saudiya,Sheikh Abdulaziz al-Sheikh wanda ya dora laifi akan alhazan yace kasarsa tayi iyaka kokarinta wajen ganin an gudanar da aikin hajjin bana ba tare da tashin hankali ba.

Haka shima yarima Sultan bin Abdulaziz da ministan harkokin cikin gida sun dora wannan laifi akan alhazan da suka taho wajen jamra dauke da kayaiyakinsu da kuma wadanda suka yi watsi da shawarar da aka basu cewa zasu iya jifa a kowane lokaci.