1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin shugabannin hukumomin tsaro a Nijeriya

September 8, 2010

Jonathan ya yi garambawul ga shugabannin rundunar soji da na 'yan sanda da kuma hukumar leken asiri

https://p.dw.com/p/P7Ho
Hoto: AP

Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin tsaron ƙasar, waɗanda suka haɗa da na 'yan Sanda da soji da kuma na hukumar leƙen asirin ƙasar, gabannin manyan zaɓukan ƙasar da za su gudana a cikin watan Janairun baɗi - idan Allah ya kaimu. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban, ta bayyana sunan Air Marshal O. O. Petirin a matsayin sabon babban hafsan tsaron ƙasar. Manjo Janar O. A Ihejirika shine sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, a yayin da Rear Admiral O.S. Ibrahim kuwa zai jagoranci sojin ruwa, kana Air Vice Marshal Umar ya shugabanci dakarun sama .

Sanarwar ta ƙara da cewa Hafiz A. Ringim shi ne zai kasance shugaban riƙon kwarya na 'yan sandan ƙasar, a yayin da Ita Ekpeyong kuwa ke matsayin Darekta Janar na hukumar leƙen asirin ƙasar..

Ofishin shugaban ƙasar ya sanar da naɗin muƙaman ne yini ɗaya kachal bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar da jadawalin zaɓuka, kana shugaban ya sanar da taron wasu gwamnoni cewar, zai tsaya takarar shugabancin ƙasa, tare da cewar a ranar 18 ga watan Satumbar nan ne zai bayyana ƙudurin hakan a bainan jama'a.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita Yahouza Sadisou