1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schäuble na ganawa da takwarorinsa na jihohin tarayya.

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubp

A yau ne ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang Schäuble, ya buɗe wani taro a birnin Nürnberg, inda zai yi shawarwari da takwarorinsa na jihohin tarayya 16, a kan shirin da gwamnatin tarayya ke niyyar gabatarwa, na bai wa baƙi kusan dubu ɗari 2 da suka daɗe suna zaune a nan Jamus takardar izinin zama. Tuni dai, wasu daga cikin jihohin tarayyar sun bayyana adawarsu ga shirin, kuma sun lashi takobin yi masa babakere a majlisar mashawarta, saboda ganin da suke yi na cewa, hakan zai ƙara musu wani sabon nauyi ne a fannin kula da jin daɗin jama’a

Shirin dai, ya tanadi bai wa baƙin da suka shafe a ƙalla shekaru 8 suna zaune bisa ƙa’ida a nan ƙasar ne takardar izinin zama na dindindin, muddin sun nuna cewa za su iya kula da kansu, ba tare da dogaro kan hukumomin bai wa jama’a agaji ba.