1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schäuble:Turkiya ta gaggauta janye kalaman batanci

Yusuf Bala Nayaya
March 7, 2017

Bayan da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya kwatanta mahukuntan Jamus da yin salon mulki irin na 'yan Nazi ne babban jami'in gwamnatin Jamus Wolfgang Schäuble ya nemi da a janye kalaman.

https://p.dw.com/p/2Yn5D
Deutschland Finanzminister Wolfgang Schäuble beim EBC in Frankfurt am Main
Hoto: Getty Images/AFP/D. Roland

Ministan kudi mai karfin fada a ji a Jamus ya bayyana cewa domin kauce wa kara shiga takun saka tsakanin mahukuntan Ankara da birnin Berlin kamata ya yi Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya janye kalaman batanci na kwatanta mahukuntan kasar da masu mulki irin na 'yan Nazi.

Huldae dipolomasiya dai ta yi tsami tsakanin kasashen na Turkiya da Jamus a baya-bayan nan lokacin da Turkiya ta rika shirya taruka na siyasa don neman karin karfi iko ga Shugaba Erdogan, tarukan da aka shirya a kasar Holland da Jamus, kasar ta Jamus dai na soke tarukan da ta bayyana da cewa bisa dalilan tsaro ne. 

Ministan kudin na Jamus Wolfgang Schäuble, mashawarci na kusa ga Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya fada wa manema labarai a  ranar Talatan nan cewa bukatar hakan ta fito ne daga shugabar gwamnatin kasar.Ya ce zai zamo dabara ga Shugaba Erdogan cikin hanzari ya karbi wannan shawara ta janye kalaman nasa cikin hanzari.