1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schröder a Turkiyya

October 12, 2005

Shugaban gwamnati mai barin gado Gerhard Schröder zai halarci liyafar bude baki a Turkiyya

https://p.dw.com/p/BvYt

Rahotanni daga kasar Turkiyya sun ce wannan shi ne karo na farko da wani P/M kasar Turkiyya ya gayyaci shugaban gwamnatin wata kasa da ba ta musulmi ba domin halartar liyafar bude bakin azumin watan ramalana. Wannan alfarmar da Türkiyya tayi wa Schröder na da nufin bayyana cikakkiyar godiya dangane da goyan bayan da ya bata a kokarinta na neman shigowa inuwar kungiyar tarayyar Turai.

Wannan cikakken aboki ne na-gari wanda ke kaunar Turkiyya tsakanin da Allah. Bugu da kari kuma shugaban gwamnati ne da ya san makama.

Wannan bayanin dai an ji shi ne daga bakin wani Bayahude dan kasuwa mai suna Ishak Alaton a birnin Istanbul. Ko shakka babu kuwa a ganawar da zasu yi da P/M Recep Tayyip Erdogan dukkan jami’an siyasar biyu zasu sha fama da radadin bankwana a zuciyarsu. Domin kuwa Schröder babban aminin Erdogan ne in ji Cüneyd Zapsu mashawarcin P/M Turkiyya a manufofin ketare, wanda ya ci gaba da bayani yana mai cewar:

Bisa ga dukkan alamu jami’an siyasar biyu na fahimtar juna sosai da sosai, duk kuwa da cewar ba kai tsaye suke musayar yawu tsakaninsu ba sai sun hada da tafinta. Amma duk da haka an samu kyakkyawar kusantar juna tsakaninsu.

Wani abin da kasar Turkiyya ke yaba wa Schröder da ministansa na harkokin waje Joschka Fischer shi ne goyan bayan da suka ba wa kasar a kokarinta na neman shigowa inuwar Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da la’akari da sabanin da ake yi akan manufofinta na cikin gida ba. A halin yanzun dai an gabatar da matakin shawarwarin karbar kasar ta Turkiyya a wannan kungiya kuma ta haka tayi watsi da adawar da jam’iyyar CDU ke yi, wacce ta fi bukatar ganin an kulla wata yarjejeniyar kawancen alfarma da kasar saboda akidarta ta Musulunci. Sai dai kuma Cüneyd Zapsu ya bayyana fatan cewar za a ci gaba da samun kyautatuwar dangantaka tsakanin Turkiyyar da Jamus a karkashin shugabar gwamnati mai jiran gado Angela Merkel. Ya ce bisa al’ada akan ji batutuwa iri dabam-dabam a yakin neman zabe, wadanda ba lalle ba ne a tabbatar da su daga bisani. Bugu da kari kuma dangantakar Jamus da Turkiyya ba kawai ta shafi KTT ba ne, akwai abubuwa da dama da suka hada kasashen guda biyu, musamman ma in an yi la’akari da Turkawa kusan miliyan uku dake Jamus.