1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SCHRÖDER YA KIRA TARON MANEMAN LABARAI A BIRNIN BERLIN.

YAHAYA AHMEDAugust 18, 2004

Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder, ya bayyana manufofin gwamnatinsa, a wani taron maneman labarai da ya kira a birnin Berlin.

https://p.dw.com/p/BvhB
Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus.
Gerhard Schröder, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus.Hoto: AP

A taron da maneman labaran da ya kira a birnin Berlin, shugaban gwamnatin tarayya, Gerhard Schröder, ya fara jawabi ne da wani dan gajeren bayani kan manufofin gwamnatinsa, dangane da harkokin tsaro da kuma na waje. Bayan haka ne kuma, ya dukufad da sauran jawabansa kan siyasar cikin gida. Cibiyar duk manufofin da gwamnatin ta tsara dai, ita ce yi wa kafofin hukuma garambawul. Shugaba Schröder ya fi nanata muhimmancin da gwamnatinsa ke bai wa canje-canjen nan ne da ake ta korafi a kansu, game da daukan matakan tsimi a fannin kula da marasa aikin yi, da kuma jin dadin jama’a. Bisa tsarin gwamnatin dai, tun daga watan Janairu mai zuwa ne, za a hade fannonin biyu zuwa kafa daya. Babu kuma wani ja da baya daga wannan shirin, inji shugaba Schröder, a lokacin da yake amsa tambayoyin maneman labarai.

Game da zanga-zangar da duk ranar litinin ake ta yi, don nuna adawa ga sabbin shirin da gwamnatinsa ta sanya a gaba kuwa, Gerhard Schröder, ya ce yana nuna fahimtarsa ga hakan, saboda ai a duk inda ake tafiyad da mulki bisa tafarkin dimukradiyya, kowa ma na da izinin bayyana ra’ayinsa. Sai dai, ya zargi jam’iyyun adawa na CDU da CSU da kuma PDS, da nuna halin munafinci, saboda kamar yadda ya bayyanar, ai tare da amincewarsu a majalisar dokoki ne gwamnati ta zartad da kudurin yi wa kafofin siyasa garambawul. Amma sai ga shi kuma, an wayi gari, su ne ma kan gaba wajen suka, a lokacin da aka zo aiwatad da manufofin. Ya dai kara da cewa:-

"Ba zan taba nuna fahimta ga wadanda ke yunkurin hana ruwa gudu a shirye-shiryen inganta halin rayuwar jama’a da muka tsara ba. Wannan sabuwar gambiza tsakanin jam’iyyun adawar CDU da CSU a bangare daya, da kuma PDS a daya bangaren, wato ba kome ba ne, illa yunkurin hana ci gaban kasarmu."

Shugaban Schrödern dai, ya dage kan matsayinsa na aiwatad da duk kuduroin da aka zartad da su a Majalisa. A nasa ganin, garambawul din na da muhimmanci kwarai ga ci gaban Jamus. Sai dai, akwai wasu marasa kishin kasa da ke yada labaran karya a bainar jama’a don tsoratad da su:-

"Mun dai yi imanin cewa, a karrshe gaskiya za ta tabbata. Kuma wannan garambawul din, zai taimaka wajen tabbatad da ci gaba mai dorewa a kasarmu, da kuma samar mata kyakyawar makoma. Sabili da haka ne kuwa, ya kamata mu yi duk iyakacin kobarinmu wajen ganin cewa, mun cim ma wannan gurin. Ba mu dai da wani zabi, face zage dantse, mu kammala wannan aikin da ke gabanmu."

Game da siyasar harkokin waje kuwa, shugaba Schröder ya nanata sha’awar da Jamus ke yi ne, ta neman samun kujerar dindindin, a kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya. Ya kara da cewa:-

"Mun dai sha bayyana matsayinmu da kuma sha’awarmu ta ganin cewa, kasashen Latin-Amirka, da na Afirka da kuma na Asiya, sun kara samun muhimmanci a kafar ta Majalisar dinkin Duniya. Kamata ya yi dai, a yi wa Majalisar garambawul, inda bayan haka, muke kyautata zaton cewa, Jamus ma za ta sami kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar. Hakan kuwa abu ne mai yiwuwa, idan aka yi garambawul din, don fadada majalisar."

A karshe dai, shugaba Schrödern ya ce, bai ga wata jibinta da shirin da Amirka ke yi na janye dakarunta daga nan Jamus da adawar da Jamus ta nuna game da yakin Iraqi ba, duk da nanata hakan da wasu bangarori ke yi.