1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schulz ne dan takarar SPD a zaben Jamus

March 19, 2017

Daukacin wakilan jam'iyyar SPD ta Jamus sun amince da Martin Schulz a matsayin wanda zai kalubalanci Angela Merkel a zaben 'yan majalisa da na shugabancin gwamnati na Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/2ZVmi
Deutschland SPD-Bundesparteitag in Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Tsohon shugaban majalisar tarayyar Turai Martin Schulz ya zama dan takarar jam'iyyar SPD da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu a zaben shugabancin gwamnatin Jamus da zai gudana a watan Satumba mai zuwa. Daukacin wakilan da suka halarcin babban taron da jam'iyyar ta gudanar a birnin Berlin ne suka kada kuri'ar amincewa da dan takarar mai shekaru 61, lamarin da ke zama farau a tarihin siyasar Jamus.

A daya hannun kuma Shulz ya maye gurbin Ministan harkokin waje kana mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel a mukamin shugaban jam'iyyar SPD da ke da matsayi na biyu a yawan magoya baya. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar da baya-bayannan ta nunar da cewar farin jini wanda zai kalubalanci Merkel ya kamo na shugabar gwamnati biyo bayan adawa da Jamusawa ke nunawa da shirin gwamnati na bude kofofi ga 'yan gudun hijira.

Martin Schulz ya yi alkawarin daidaita albashi tsakanin maza da mata, tare da kara tallafi ga wadanda suka rasa gurabensu na aiki.