1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Schulz ya soki Merkel da rashin hangen nesa

Abdul-raheem Hassan
September 16, 2017

Yayin da aski ke kara zuwa gaban goshi a zaben Jamus, dan takarar jam'iyar SPD mai adawa Martin Schulz ya bukaci al'ummar kasar da su fahimci alkiblar kyakkyawar shugabanci da zai dore.

https://p.dw.com/p/2k79v
Würselen Martin Schulz vor Wahllokal zur Bundestagswahl
Hoto: Reuters/T. Schmuelgen

Dan takarar jam'iyar adawa ta SPD Martin Schulz da ke zama babban abokin hamaiyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a babban zaben kasar da ke tafe, ya caccaki manufofin da shugabar da rashin salon iya mulki da kuma rashin hangen nesa,

 "Angela Merkel tana shugabancin Jamus a kan manufofin zaman lafiya da more rayuwa. Tabbas ta yi gaskiya, domin muna zaune a kasar lafiya kuma muna jin dadi, to amma muna bukatar ingantacciyar rayuwa mai nagarta da za ta dore a nan gaba. Wannan ya sa muke bukatar bayyana wa al'umma manufofin da muka sa gaba."

A wata ganawa ta musamman da DW, a yayin gangamin yakin neman zabe a birnin Frieburg da ke yammacin Jamus, Schulz ya kuma yi kakkausar suka kan shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan bisa 'yan gudun hijira yana mai cewa ba zai rusuna wa Erdogan ba, kuma ba zai amince da duk wani kokari na yi wa Jamus zangon kasa da batun 'yan gudun hijira ba.