1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Serkan Tören, wakilin majalisar Bundestag ɗan usulin Turkiya

Tijani LawalOctober 27, 2009

Serkan Tören, ɗan usulin Turkiyya na daga cikin wakilan majalisar dokokin Jamus tsattsan 'yan kaka-gida

https://p.dw.com/p/KGmT
Serkan Tören, ɗan jam'iyyar FDPHoto: FDP

A yau talata aka gabatar da zaman farko na sabuwar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. A tsakanin wakilan majalisar su 622 akwai wasu goma sha takwas, waɗanda aƙalla ɗaya daga cikin iyayensu ke da tushe na ƙetare, kamar dai wakilin jami'iyyar Free Democrats Serkan Tören, wanda iyayensa suka fito daga Turkiyya.

A shekara ta 1993 ne Serkan Tören ya shiga ƙarkashin tutar jam'iyyar Free Democrats ko kuma FDP a taƙaice. A wancan lokaci yana ɗalibci ne a jami'ar Hamburg a ƙarƙashin wani shahararren farfesa ɗan jam'iyyar ta FDP dake da ƙwarewa akan dokoki na ƙasa:

"A wancan lokaci ana batu ne akan haƙƙin farar hula da na ɗan-Adam da 'yancin walwala. Wannan maganar tayi tasiri a kai na. Daga nan na tsayar da shawarar zama memba a jam'iyyar FDP."

Shi dai Serkan Tören an haife shi ne a Fatsa, wani ɗan ƙaramin garin dake gaɓar tekun bahar-aswad a Turkiyya. Yana ɗan watanni goma kacal da haifuwa iyayensa suka yiwo ƙaura zuwa garin Stade dake arewacin Jamus tare da sauran 'yan uwansa. A garin mai arzƙin masana'antu dake da tazarar kilomita 45 daga birnin Hamburg Serkan Tören ya fara zuwa makarantar renon ƙananan yara sannan ya shiga faramare. Gaba ɗaya a wannan garin yayi yaranta kuma har yau yana da abokai a can:

"Stade tamkar gida ne a gare ni, saboda mutane sun karɓe ni da hannu biyu-biyu. Ala-kulli halin ya kan ɗauki lokaci kafin mutum ya saba da sauran jama'a, saboda mazauna arewacin Jamus, ba kasafai ba ne suke marhabin lale da mutum. Amma da zarar an fahimci juna, zaka ga 'yan arewacin Jamus amintattun mutane ne."

Serkan Tören na miƙa cikakkiyar godiyarsa ga iyayensa, waɗanda ya ce su ne suka ba shi cikakkiyar dama ta neman ƙarin ilimi har ya zama lauya kuma yau ya wayi gari a matsayin wakili a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. Iyayen nasa sun sha nanata ma sa cewar in har yana fatan samun ci gaba a rayuwarsa a Jamus wajibi ne yayi hoɓɓasa a makaranta ya kuma cakuɗa da takwarorinsa Jamusawa. Ta la'akari da haka jami'in siyasa ke tattare da imanin cewar ta hanyar ilimi ne kawai 'yan kaka-gida zasu samu kyakkyawan ci gaba a harkokin rayuwa ta yau da kullum a ƙasar ta Jamus:

"Akwai cikakkiyar dama ta neman ilimi kama daga faramare har zuwa jami'a. Amma alhakin lamarin ya rataya ne a wuyan iyayen yara da su yi amfani da wannan dama. Ba shakka akwai buƙatar gayara a ɓangaren ilimi, amma bai kamata neman ilimin ya danganta da tushen mutum ba."

To sai dai kuma lamarin ya banbanta a ɓangaren siyasa, kamar yadda Serkan Tören ya nunar. Domin kuwa ko da yake yawan Jamusawa dake da tushe daga ƙetare ya kama kashi 10% na illahirin al'umar ƙasar, amma duka-duka yawan wakilansu a majalisar dokoki bai zarce kashi 3% ba:

"Wannan adadin bai taka kara ya karya ba. Kuma bai yi daidai da taswirar al'umar ƙasa ba. A saboda haka wajibi ne mu yi gayara. Wajibi ne 'yan kaka-gida da tsattsan su su ƙara kutsawa a harkokin siyasa. Sannan su kuma jam'iyyun siyasa wajibi ne su riƙa tuntuɓar 'yan kaka-gida domin shawo kansu su shiga harkar siyasa."

Jami'in siyasar na taka muhimmiyar rawa a wannan fannin a wasu ƙungiyoyi na Turkawan dake Jamus duk da banbance-banbancen manufofin siyasa dake akwai tsakanin ɗaiɗaikun 'ya'yan ƙungiyoyin.

Mawallafi: Kouparanis/Ahmad Tijani Lawal

Edita:Umaru Aliyu