1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shaánin tsaro na kara tabarbarewa a Sri Lanka

August 17, 2006

An yi mummunan dauki ba dadi tsakanin yan Tawayen Tamil Tigers da jamián tsaro na Gwamnati.

https://p.dw.com/p/Btyf
Ana cigaba da fuskantar tashin hankali a Sri Lanka
Ana cigaba da fuskantar tashin hankali a Sri LankaHoto: AP

Bayanai daga ƙasar Sri Lankan na cewa an yi ƙazamin barin wuta tsakanin dakarun sojin gwamnati da yan tawayen na Tamil Tigers. Wata majiya daga sojin ƙasar ta ce an kashe a ƙalla yan tawaye 70 a fafatawar da suka yi ta tsawon dare. Majiyar ta ce a tsawon makon da ya gabata an kashe a ƙalla yan tawayen fiye da dari daya a garin Jaffna. Tun ma dai kafin ɓarkewar wannan rikici yankin na Jaffna na cikin wani yanayi sakamakon taɓarɓarewar alámura a yaƙin basasar da yankin ya sha fama da shi har tsawon shekaru ashirin.

A halin da ake ciki babu kyakyawar hanya zuwa cikin gari yayin da dukkanin turakan wuta dana wayar tarho duk aka ragargaza su. Kimanin mutane 800 ne suka rasa rayukan su a cikin wannan shekarar bayan ɓarkewar faɗan baya-bayan nan a sakamakon rashin jituwa a dangane da hanyar ruwa. Jamiín ƙasar Norway Manjo janar Ulf Henricsson wanda ke jagorantar tawagar dake lura da yarjejeniyar tsagaita faɗa a tsakanin gwamnati da yan tawayen Tamil Tigers, yace idan baá sami ɓangarorin biyu sun martaba yarjejeniyar tsagaita wutar ba, zaá cigaba da hasarar rayukan jamaá masu ɗumbin yawa. Yace a zahirin gaskiya yarjejeniyar tsagaita wutar sam bata aiki, hasali ma dukkan ɓangarorin biyu basa martaba yarjejeniyar, basu ma kuma damu da ita ba. Garin Jaffna wanda ke zama mahaifar da yawa daga cikin manyan shugabannin yan tawayen kuma cibiyar yaƙin da suke na mallakar yankin ƙabilar Tamil ya kasance a datse daga sauran yankin Tamil.

Rahotanni dai na cewa a sakamakon tabarɓarewar harkokin tsaro ya zama wajibi ga jamián lura da shirin samar da zaman lafiya a gabashin Sri Lanka su tattara ya nasu ya nasu bayan da aka kusa kai musu hari a ɓarin wuta tsakanin yan Tawayen da jamián tsaro. Wani mai magana da yawun ƙungiyar kula da shirin zaman lafiyar Thorfinnur Omarsson yace ya zama wajibi su janye mazaunin su daga lardin Trincomalee zuwa wani yanki mai tazarar kilomita 50 a gabashin ƙasar.

Shi kuwa kakakin maáikatar tsaro ta ƙasar Sri Lankan, Rambukwalle ya zargi yan tawayen Tamil Tigers ne da ƙara jefa alúmomin yankin cikin matsanancin hali. Jamiín yace a yayin da yan tawayen suke ƙara jefa ƙasar cikin yanayi na yaki, suna kuma jefa rayuwar alúmar cikin mawuyacin hali, to amma a ɓangare guda gwamnati na ƙoƙarin samar da wani tsari da nufin biyan buƙatun tsirarun ƙabilun.

Wani babban jamií kuma mataimakin sakatare a maáikatar harkokin wajen Amurka Steven Mann na fatan ganawa da shugaban ƙasar Sri Lanka Mahinda Rajapakse domin tattauna yanayin da ƙasar ke ciki, sai dai a hannu guda ƙasashen duniya basu bada wata kulawa ba sosai a game da tabarɓarewar alámura a ƙasar ta Sri Lanka. Hatta ƙasar India wadda ke maƙwabtaka da Sri Lankan ta ƙi yarda ta tsunduma kan ta cikin rikicin.

Jakadu dai na zargin ƙungiyar Tamil Tigers da tada yamutsin na baya bayan nan yayin da a waje guda kuma gwamnati ta Sri Lanka wadda ta kai iya wuya bata, son janyewa ko kuma nuna gazawa wajen yaki da yan tawayen. Har yanzu akwai rudani a ƙasar a game da farmakin jiragen sama da aka kai wani gidan marayu wanda ke maƙare da ƙananan yara yan makaranta da kuma ya yi sanadiyar mutuwar yara da dama. Gwamnati ta yi zargin cewa gidan sansani ne na yan tawayen Tamil Tigers. Jamián masu lura da zaman lafiya a ƙasar sun ce sun ga gawarwakin yara goma sha tara, yayin da yan Tamil ɗin suka ce yara 60 ne suka mutu.