1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sha´awar mallakar makaman nukiliya.

Mohammad Nasiru AwalFebruary 6, 2004
https://p.dw.com/p/Bvm2
A tsakiyar watan janeru hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ba ta yi kuskure ba wajen tabbatar da cewa kasar Libya ta nisan ta kanta daga shirin kera makaman nukiliya. A dai halin da ake ciki wannan kasa ta dakatar da dukkan shirye-shiryenta na nukiliya. Amma bisa ga dukka alamu, kasar Iran ta yi nisa a shirinta na nukiliya, ko da yake ta nunar da cewa shirinta na makamashi ne amma ba makamin nukiliya ba.

Duniya ta dade tana jin irin wadannan zantuttukan musamman daga kasashe KTA da Pakistan. A jerin wadannan kasashen dai kasar KTA ce ta ke kan gaba wajen kera bama-baman nukiliya. Yayin da ita kuma kasar Pakistan tuni ta kera har ma ta yi gwajin irin wadannan makamai a cikin shekarun 1990. Haka zalika wannan kasa ta sayarwa kasashe kamar su KTA da Iran da kuma Libya fasahar kera makaman nukiliya. Wai mai zai hana wadannan kasashe da yammacin duniya ke yi musu lakani da matattarar ´yan ta´adda, hada kai a kokarinsu na kera makaman nukiliya? In dai hukumomin leken asiri na kasashen yamma na mamakin hakan a yanzu, to kenan sun shafe shekaru kusan 20 suna barci ko kuma suna so su kawad da kai ne daga wata gazawarsu.

A cikin shekarun 1980, Pakistan ta kasance babbar kawar kasashen yamma, musamman lokacin da ake dab da kawo karshen yakin cacar baka. An dai dauki matakai daban daban don hana TS samun gindin zama a Afghanistan, wanda hakan ya kai ga taimakawa Pakistan a fannen soji, hade da kera bama-baman nukiliya da kuma sayar da su a ketare. A game da kasar KTA kuwa irin cinikin nan ne na ba ni gishiri in ba ka manda. Inda ta yi musayar fasahar nukiliya da ta kera rokoki. Libya kuwa ta kashe makudan kudade wajen sayen wannan fasaha daga kasar Pakistan, amma hakan ta bai cimma ruwa ba.

To wai shin mai yasa kasashen yankin GTT ke da sha´awar mallakar bama-baman nukiliya ne? Babban dalili dai shine don su kasance ba masu dogaro da manyan daulolin dunia kamar Amirka ba. Wani dalilin kuma shine kasancewar kasar Isra´ila ita ce babbar daula a wannan yanki kuma bisa ga dukkan alamu tana mallakar kanun makaman nukiliya kimanin 200, jama´a a yankin na GTT na daukar ta a matsayin babbar barazana.

Kamata yayi matakan da shugaban Libya Muammar Ghaddafi ya dauka na yin watsi da shirinsa na nukiliya, su karfafawa kasashen Amirka da na Turai guiwa wajen haramta ko wane irin shiri na kera makaman kare dangi a GTT. Amma idan aka ci-gaba da sa ido akan kasashen Larabawa ko na musulmi kadai, amma ita kuwa Isra´ila aka kyale ta, to ko shakka babu wasu kasashe zasu bi ta wata hanya don mallakar makaman na nukiliya. Amma idan aka nuna adalci, to za´a hana wadannan makaman fadawa hannun ´yan ta´adda.