1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soziale Netzwerke

August 18, 2010

Ko me nene ma'anoninsu ? Ko kuma yaya suke ai, kuma ta wace hanya ne suke samun kuɗaɗen shiga.

https://p.dw.com/p/OqaG

A dai shekarun da suka gabata an ba da ma'anoni da dama ga shafukan Internet irinsu facebook da Myspace da kuma Xing da ke zaman dadalin ƙulla ƙawance da sada zumunci.

Shafukan kulla kawance da sada zumunci a duniya sai kara samun bunkasa suke yi dubi ga miliyoyin masu amfani da yanar gizo dake kara yin turuwa domin shiga wadannan shafuka. Ko shakka babu wadannan shafuka na kara samun karɓuwa.

A bisa ka'ida dai waɗannan shafuka suna amfani da salo iri guda. Ana amfani da su wajen domin samun katin zama mambobi tare da kuma samun damammaki daban-daban ta amfani da adireshin juna. Duk wanda ya so yin rejista to wajibi ne ya ba da bayani game da shi kansa . Ko da yake ana yin hakan ne kyauta amma kuma ya zamo wajibi mutun ya ba da sunansa da kuma wasu sirri na shi kamar adireshin E-Mail ko kuma ranar haifuwa. To amma ba tilas ne mutun ya ba da hotonsa ba, ko da yake wasu su kan yi hakan.

XING Screenshot
Hoto: XING

A baya ga haka mutun zai iya taskance abubuwa da dama a ƙarƙashin adireshinsa: misali abin da yake son yi a lokacin hutunsa, litattafai dake burgeshi da kuma hotunan da filim-filim. To sai dai kowane shafi na da yadda yake tafiyar da wannan dama ta tasakace abubuwa. Alal misala a shafin Xing mutun zai iya daukar bayanai game da tallace tallace . To amma kuma bisa wasu dalilai mutun zai iya tsai da shawara game da abin da yake son wani ya gani da kuma waɗanda abokansa ne kadai za su iya gani.

Sai kuma fannin neman bayanai da mamba za iya yin amfani da shi domin neman abokan arziƙi da kuma waɗanda ya sani, domin aike musu tambayoyin sada zumunci. Mutun na samun damar yin amfani da shafin ne da zaran ya sanya mabuɗinsa na sirri. A dai halin yanzu ana samun wannan damar ta jerin adireshin da aka adana a wayar salula.

Daga nan ne mutun ke sanin wanda ya fara yin rejista a matsayin abokinsa da kuma ra'ayoyi game da abokantaka . A nan ne mutun zai samu shafuka da dama na facebook waɗanda daga garesu zai samu mambobi da zai iya kulla ƙawance da su. Ta haka ne ake samun bunƙasa wannan fasaha ta sada zumunci a cikin gaggawa.

Twitter DW Logo

A dai halin yanzu Facebook ne ke kan gaba tsakanin waɗannan shafuka-A watan Yulin wannan shekara facebook ya samu sabbin mammobobi guda miliyan ɗari biyar. A dai watan Fabarairun shekarar 2004 ne dai, Mark Zuckenberg da haɗin-gwiwar abokan karatunsa a jami'ar Harvard ya kirkirar da wannan shafi

Shafin Myspace shi kuma ya daɗe yana doke saura a yawan mambobi daga kasa da kasa ko kafin Facebook ya tsere masa a shekarar 2008. Mawaka da sauran masu fasahohi daban daban sun gwammace yin amfani da Myspace. Sai kuma shafin Xing da aka kirkirar a nan Jamus da ke zaman dandalin samun adireshi na abokan ciniki.

Daga tallace-tallace ne waɗannan shafuka ke samun kuɗaɗen shiga ko da yake mambobi na rejista ne kyauta. To sai dai ana rashin bayanai game da yadda ake kimanta bayanai game da masu rejista.

Mawallafiya: Halima Abbas Edita: Zainab Mohammed