1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shagulggullan karamar salla a kasashen musulmi na dunia.

November 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvMf

Bayan wata guda na ibadar azumin Ramadan yau ne a kasashe da dama, musulmi ke shagulgullan salla karama.

A mafi yawan kasashen Larabawa, da wasu kasashen musulmi na Afrika, da su ka hada da Gambia, Senegal, Guinee da dai sauran su an yi sallar idi a sahiyar yau cikin nishadi da farin ciki.

A wasu kasashen kuma kamar su Taraya Nigeria Jamhuriya Niger Mali da Libia, tun jiya a ka yi salar ta idi, a na kuma ci gaba da shagulugulla a yanzu haka.