1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shagulgulan Ranar Sake Hadewar Jamus

October 4, 2004

A jiya lahadi ne aka gabatar da shagulgulan bikin sake hadewar Jamus a duk fadin kasar ko da yake bikin da ya fi daukar hankali shi ne wanda aka gudanar a garin Erfurt tare da halarcin shugaban kasa Horst Köhler da shugaban gwamnati Gerhard Schröder da sauran gaggan jami'an siyasar kasar

https://p.dw.com/p/Bvg0
Shagulgulan bikin sake hadewar Jamus
Shagulgulan bikin sake hadewar JamusHoto: AP

A cikin jawabin da ya gabatar a dandalin bikin da aka tsayar a farfajiyar shelkwatar karamar hukumar garin Erfurt, shugaban kasar Jamus Horst Köhler yayi bayani dalla-dalla a game da abubuwan da yake da imanin cewar zasu iya taimakawa wajen kara samar da kusantar juna tsakanin jamusawan gabaci da na yammacin kasar. Köhler ya ci gaba da cewar:

Wajibi ne mu yi bakin kokarinmu wajen samar da guraben aiki ga jama’a, wannan ita ce manufa mafi a’ala da ya kamata ta kasance a gabanmu. Akwai bukatar samar da aiki ga kowa da kowa da daga matsayin ilimi da nagartattun matakai na gwamnati da kuma sabunta tsarin zaman tarayya a nan kasar. Wadannan abubuwa guda hudu sune zasu taimaka a fita daga mawuyacin hali na kaka-nika-yi da ake ciki yanzun. Ko da yake ba su ne kadai ya kamata a ba da la’akari da su ba, amma fa suna da muhimmanci akan manufa.

Bisa ga ra’ayin shugaban kasa Horst Köhler Jamus gaba dayanta ke bukatar canje-canje da sabunta al’amuranta, amma ba yankin gabacin kasar kadai ba. A lokacin da ya waiwayi baya, yayi nuni da cewar tsofon shugaban gwamnatin Jamus ta Yamma Helmut Kohl da P/M JTG na da Lothar de Maiziere sun gaggauta daukar matakan sake hadewar Jamus a shekara ta 1990. Amma fa babu daya daga cikinsu ko wani jami’i na gwamnati, abin da ya hada har da shi kansa a matsayinsa na karamin minista a ma’aikatar kudi, yayi karatun mun natsu domin hangen nesa, ballantana a dauki nagartattun matakai na garambawul da aka dade ana sauraron samuwarsa a yammacin Jamus.

A nasa bangaren gwamnan jihar Thurinjiya dake karbar bakuncin shagulgulan bikin sake hadewar yayi kira ga jami’an siyasa da ‚yan kasuwa da su hakura su kuma nuna halin sanin ya kamata dangane da zanga-zangar da ‚yan gabacin Jamus suka rika yi a watannin baya-bayan nan domin adawa da manufofin garambawul ga kasuwar kodago, abin da ya kai su har da ba wa masu zazzafan ra’ayin kyamar baki da wariyar jinsi goyan baya a zabubbukan majalisun jihohin Sachsen da Brandenburg. Ya ce yankin gabacin Jamus ya fuskanci canje-canje masu yawa a shekarun baya-bayan nan kuma jama’a ba zasu yarda su ci gaba da zama ‚yan rakiya a wannan yanki ba, inda yawan marasa aikin yi ya ribanya na yammacin Jamus. Wannan zanga-zanga da sakamakon zabubbukan tamkar gargadi ne ga ‚yan siyasa. Dukkan masu gabatar da jawabai a lokacin shagulgulan, abin da ya hada har da shugaban gwamnati Gerhard Schröder sun yi tsokaci da tabarbarewar tsarin zamantakewar jama’a sakamakon matsalar rashin aikin yi da kuma rashin hangen wata kyakkyawar makoma.