1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shagulgulan Sallah a kasashen Larabawa

Mahmud Yaya Azare
June 26, 2017

A ranar Litinin (26.6.2017) wasu kasashen Larabawa suka gudanar da bukukuwan Sallah bayan da galibin kasashen yankin su kai tasu Sallar a ranar Lahadi kamar yadda ya ke a wasu kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/2fQil
Libyen Id al-Fitr Fastenbrechen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Kasashen Oman da Iran da Libiya da Maroko da yankin mabiya Shi'a a kasar Iraki na daga cikin wadanda su ka yi ta su Sallar a ranar Litinin, yayin da sansanonin 'yan gudun hijira a yankin Mosul na kasar Iraki suka yi ta su a ranar Lahadi cikin halin matsatsi da zakuwar ganin an gama fatattakar 'yan kungiyar IS don samun damar komawa gidajensu.

Syrien Präsident Bashar al-Assad
Saboda bukukuwan Sallah Karama, shugaban Siriya ya yi daruruwan fursunoni afuwa ciki kuwa har da mataHoto: picture alliance/dpa/Syrian Arab News Agency

A kasar Siriya kuwa shugaban kasar Bashar al-Assad a karon farko tun bayan soma bore ya yi Sallar Idi a garin Hama da ke zama tungar masu tayar da kayar baya, yara kanana a garin sun yi ta yin shagulgulan Sallah ba tare da fargabar fadowar rokoki a kansu ba. Sannan sakin fursunonin yaki 670 cikinsu har da mata 91 da shugaba Assad ya yi wa afuwa ya sa 'yan uwansu kukan murna don auna sa'ar da suka yi.

Yemen Id al-Fitr Fastenbrechen
Annobar kwalara da yakin da ake yi ya dakushe armashin bikin Sallah a kasar YemenHoto: Getty Images/AFP/M. Huwais

A kasar Masar kuma tsadar rayuwa ta ragewa bukuwan Sallar armashi duk kuwa da sako fursunonin da suka tafka barna da kuma wasu da ke fama da jinya da mahukunta suka yi.

Can a Yemen inda annobar cutar kwalarar da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba a taba ganin irinta a duniya ba ta shafi jin dadin masallata. Matsalar dai ya zuwa yanzu ta halaka kimanin rayuka 1,300 baya ga yakin basasar da ake ciki. Wadannan lamuran sun hadu sun dagula rayuwar al'ummar kasar. 'Yan kasar sun yin amfani da bukukuwan Sallar wajen jajantawa juna da fatan Allah ya kawo karshen matsalolin da suke fuskanta.