1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shakku kan ƙuri'ar raba gardama a Sudan

July 31, 2010

Ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun fara tantama a kan yiwuwar gudanar da ƙuri'ar raba gardama tsakanin arewaci da kudancin Sudan

https://p.dw.com/p/OYwU
Salva Kiir, shugaban gwamnatin kudancin Sudan, yana rungumar wani jami'in soja bayan jawabin karɓar aiki a wa'adi na biyuHoto: AP

A yayin da lokacin da aka tsayar don gudanar da ƙuri'ar raba gardama a Sudan ke ƙara kusantowa, ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama, sun ce rashin cikakken shiri don tunkarar wannan lokaci, wani abin a duba ne domin tabbatar da ganin ƙasar ba ta sake fuskantar wani yaƙin basasa ba.

Tun dai a cikin shekara ta 2005 ne ɓangarorin arewaci da kudancin Sudan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yin ƙuri'ar raba gardama domin 'yantar da kudancin ƙasar mai ɗimbin arzikn ma'adanai daga arewacin Sudan. Al'ummar kudancin ƙasar ta Sudan da mabiya addinin kirista suka fi rinjaye na zargin arewacin ƙasar da Larabawa musulmi suka fi yawa da nuna musu ƙabilanci tare da mayar da su bayi. Wannan al'amari ne ya jefa ɓangarorin biyu cikin yaƙin basa da aka shafe shekaru 20 ana yi, wanda ba a cim ma matsaya ba sai bayan yarjejeniyar ta 2005.

Silver Kirr shi ne mataimakin shugaban ƙasar Sudan ƙarƙashin gwamnatin haɗaka da ake aiwatarwa yanzu haka a ƙasar tsakanin kudanci da arewaci, ya ce yana da yakinin za a samu nasarar aiwatar da wannan ƙuri'ar raba gardama.

"Ƙarƙashin wannan yarjejeniya dukkanin ɓangarorin biyu mun amince za mu tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar yin ƙuri'ar raba gardama, ga shi kuma lokaci na ƙaratowa, don haka ya zama mana dole mu yi tsayuwar daka wajen ganin an aiwatar da haka ba tare da fuskantar wata matsala ba. Ina kuma sa ran za a aiwatar da wannan yarjejeniya da muka sanya hannu a kanta."

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon yayi gargaɗin cewa ƙaruwar rikice rikice a yankin Darfur da kuma rashin ingantacciyar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da ƙungiyar 'yan tawaye ta Justice and Equality Movement zai iya haifar da cikas ga wannan yunƙuri na kaɗa ƙuri'ar raba gardama tsakanin kudanci da arewacin Sudan.

Sai dai kuma Silver Kirr ya ce babu wani yanayi da zai sa su 'yan kudanci su 'yantar da kansu kai tsaye saɓanin yarjejeniyar da aka ƙulla.

"Ba mu da wani buri ba ma kuma tunanin akwai wani yanayi da zai sa mu yi gaban kanmu wajen 'yantar da kudancin Sudan ba tare da bin ƙa'idojin da muka yi yarjejeniya ba."

Yanzu dai duniya gaba ɗaya ta zuba ido a kan wannan batu na yin ƙuri'ar raba gardama don duba yiyuwar 'yantar da kudancin ƙasar da aka tsara gudanarwa a cikin watan Janairun 2011.

A hannu guda kuma ƙungiyoyin kare hakkin Bil Adama na yin kira ga ƙungiyoyin da ƙasashen da suka yi alƙawarin ba da tallafi don tabbatar da ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya, waɗanda suka haɗa da Tarayyar Afirka da MƊD da Tarayyar Turai da Amurka, su taimakawa Sudan wajen aiwatar da yarjejeniyar ta 2005.

Mawallafiya: Halima Sani

Edita: Mohammad Nasiru Awal