1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi akan matsalolin Nuclear a 2006

Zainab A MohammedDecember 28, 2006

Idan har baa cimma warware takaddama data dabaibaye batun makaman nuclear ba a shekarata ta 2006 mai karewa ba,babu shakka sabuwar shekara ma bazata kai labari ba adangane da shawo kan wannan matsala.

https://p.dw.com/p/Btwq
Ahmadinejad na Iran
Ahmadinejad na IranHoto: DW
A watan oktoba 2006,shekaru 8 bayan India da pakistan sun tsallake bakin kofa da rikicin nucleansu,an sake wayan gari da wani sabon rikici,lokacin da Koria ta arewa ta harba boma boman Atom tare da ikirarin kanta a matsayin kasa dake da makamin nuclear.Tattaunawar shawo kan Pyangyong tayi watsi da makaman nuclear yaci tura,wanda aka mata alkawarin musayar hakan da da tallafin tsaro dana tattalin arziki,tattaunawar data rushe a makon daya gabata.

Bugu da kari shekarar ta 2006 dai ta kuma fuskanci cigaban sabanin raayi tsakanin kasashen yammaci da kasar Iran ,adangane da batun makamin nuclear da suke zargin janhuriyar ta islama da kerawa.

A yan kwanakin da suka gabata nedai komitin sulhun mdd ta kakabawa Tehran takunkumi,sakamakon wannan taurin kai dake cigaba da nunawa.A nata hannu Tehran tayi watsi da wannan takunkumi dacewa basa bisa kaida ko kadan,tare da alkawarin cigaba da sarrafa harkokin makamashinta na nuclear datakeyi.

Bugu da kari wani cigaba da aka samu a kudancin Asia ya dada ruruta wutan wannan riki da ake fama dashi,ayayinda India da Amurka suka halalta yarjejeniyar harkokin nucklear cikin shekara guda da rabi da suka gabata.Wannan yarjejeniya dai zai sanya India cikin gamayyar kasashe masu kasuwancin makamashin Nuclear,duk dacewa ayanzu kasace mai makaman nuclear,kana bata rattaba hannu a yarjejeniyar dakatar da yaduwar makaman a doron kasa ba.

A halin da ake ciki yanzu haka dai Kasashen India da Pakistan na cigaba da gwajin makaman su masu linzami ,tare da cigaban dangantakarsu a matsayin abokan gaba,duk da jerin tattaunawar sulhu dake gudana a tsakaninsu.

Rahotanni binciken da cibiyar nazarin kimiyya ta Amurka ta fitar na nuni dacewa ,kasashe 8 sun yi gwajin makamai masu linzami daban daban sama da 26,a yanayi daban daban har 24 a wannan shekarata 2006,mai karewa.Wadannan kasashe kuwa sun hadar da amurka da Rasha da Faransa da China ,baya ga India da Pakistan da Korea ta Arewa da Iran.

To sai dai manazarta nayiwa Amurka gargadin cewa tayi taka tsantsan,domin zaa kawo lokacin da kasashen da basu da wani karfi zasu kai kera makamin kare dangi da zasu harba zuwa yankunanta,musamman a yanzu da takae dada haifar wa kanta karin bakin jini a yankuna da ake fama da rigingimu da suka hadar da yankin gabas ta tsakiya.