1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi bisa karbe iko da Palmyra

Kudascheff Alexander Kommentarbild App
Alexander Kudascheff
March 29, 2016

Sojojin gwamnati Siriya sun sake kwace garin Palmyra, mai kayan tarihi abin da ke zama nasara mai matukar muhimanci ga shugaban Bashar al-Assad wanda zai bai wa magoya bayansa kwarin gwiwa.

https://p.dw.com/p/1ILQW
Russland Syrien Assad bei Putin
Hoto: Reuters/RIA Novosti/Kremlin/A. Druzhinin

A sharhin da babban editan DW, Alexander Kudascheff ya rubuta ya bayyanan cewa, tun daga 'yan makonnin baya, an rika ganin alamun cewar mayakan kungiyar tarzoma ta IS suna janyewa daga yankunan da suka kama a kasashen Siriya da Iraki, bayan kayen da suke sha daga sojojin kasashen biyu. Wannan nasara ce mai matukar muhimanci ga sojojin na Siriya saboda ta bai wa shugaba Bashar al-Assad kwarin gwiwar mayar da hankali ga neman sake kwato garin Raqqa, inda 'yan kungiyar ta IS suke da helkwata.

A game da kasar Iraki kuwa, sojojin gwamnati suna ci gaba da shirye-shiryen aukawa birnin Mosul. Idan har suka sami nasarar haka, sauran yankunan da za su rage wa 'yan kungiyar IS ba su da yawa, kuma daga nan za a fara ganin alamun rushewar kungiyar. To sai dai hakan, inji Kudascheff, ba zai canza komai ba a game da hadarin da nahiyar Turai take fuskanta na ayyukan tarzoma daga magoya bayan wannan kungiya.

Yiwuwar rushewar kungiyar IS da kawo karshen ayyukan rashin imani na kungiyar bisa sunan Musulunci da kawo karshen Khalifar da ta kafa, duk abubuwa ne da a bisa duban farko, suna iya sassauta mummunan halin rayuwa ga al'ummar Siriya da Iraki. Sakamakon nasarar da Shugaba Bashar al-Assad ya samu a Palmyra tare da taimakon Rasha, ya sanya da farko dai shugaba Assad ya sake zama mai karfin fada aji a yankin, kuma duk mai bukatar samun zaman lafiya ko kawo karshen yaki a yankin, tilas sai ya hada da goyon baya daga shugaban na Siriya.

Wannan dai mummunan abu ne ga kasar, kuma mummunan abu ne ga 'yan adawa da ke zaman hijira a ketare kuma suke da'awar dimokaradiyya. Mutumin da a tsawon shekaru biyar ya zama sanadin yakin basasa da mutuwar mutane kimanin 250.000, yanzu ya zama mai matukar muhimmanci a duk wani yunkuri na neman sulhu a rikicin Gabas ta Tsakiya. Ita ma Rasha sai ga shi karfin angizonta ya karu a duk wasu shawarwari na neman sulhu, saboda ta bai wa Bashar al-Assad damar samun nasara kan mayakan IS, saboda haka ba za ta kyale wannan dama da ta samu ta wuce ta ba.

Abin da kuwa hakan yake nufi shi ne, a hannu guda, shugaba Assad zai ci gaba a kan mulki, yayin da Rasha, duk da matsalolin tattalin arziki da take da su a gida, amma ta zama wadda tilas a yi da ita a duk wani abin da ya shafi Gabas ta Tsakiya. Hakan kuwa ba dai saboda sansaninta a Siriya ba ne, amma sai saboda ganin yadda ta zama abokiyar burmin Amirka a yankin da shugaba Barack Obama ya janye daga cikinsa gaba daya.

Kasashen Turai sun dukufa ne kawai, ga neman yadda za su shawo kan matsalolinsu na 'yan gudun hijira. Sukan zauna kan teburin shawarwarin neman sulhunta rikicin Siriya, kuma suna ba da taimako sosai a fannin tattalin arziki, amma matsayinsu bai wuce 'yan amshin shata masu jiran sanya hannu kan yarjejeniya idan ta samu ba, saboda angizonsu a al'amuran siyasar nahiyar da ke makwabtaka da su, har yanzu ba ta taka kara ta karya ba. Kasashen Ingila da Faransa, wadanda bisa al'ada suke da manufofi na kashin kansu kan Gabas ta Tsakiya, yanzu dai sun zama 'yan abi yarima a sha kida, duk kuwa da hare-haren da aka kai wa Faransa ranar 13 ga watan Nuwamba na bara.

A halin yanzu dai Bashar al-Assad shi ne ya ci gajiyar yakin da ke gudana kan kungiyar IS, su kuma Rashawa angizonsu ya karu a yankin. Amirkawa a daya hannu, sun zama 'yan kallo, musamman saboda yakin neman zaben shugaban kasar ya dauke masu hankali. Kasashen Turai suna sanya bakinsu cikin l'amarin, amma ba a yanke wata muhimmiyar shawara da su. A halin da ake ciki, ayyukan tarzoma za su ci gaba ko dai a Pakistan ko a nahiyar Turai ko a Najeriya.

Türkei Wladimir Putin und Barack Obama in Antalya
Hoto: picture alliance/AP Images/K. Ozer
09.2010 DW-TV Quadriga Moderator Alexander Kudascheff
Alexander Kudascheff, Babban editan DW