1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Hankalin duniya ya koma kan Jamus

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
June 12, 2017

Akasari ana kallon kasar bisa sha'awa da jinjinawa. Wasu na cike da mamaki, wasu na kishi, yadda Jamus ta iya dungulewa wuri guda duk da tarin kalubale da matsalolin da ta fiskanta.

https://p.dw.com/p/2eUWW
Deutschland Reichstag
Hoto: picture-alliance/R. Goldmann

Kasar ta Jamus da ma shugabar gwamnatinta Angela Merkel, duk a yanzu sune fata daya da ta saura ga makomar Turai, to amma wasu na zargin kasar da cewa tana yin iyakokarinta na dinkewar Turai ne don biyan bukatunta tattalin arziki, a matsayinta na kasar da ta fi ko wace fitar da hajoji zuwa ketare. Kana a matsyinta na wace ta yi fintikau a karfin tattalin arziki.

Aikata Alheri ko Babakere

Ya dai danganta ga inda ka kalli lamarin, wasu na cewa karban 'yan gudun hijira miliyan daya da Jamus ta yi a matsayin aikata alheri, wasu kuwa na ganin hakan kawo karshen kiristoci ne a Turai. A bisa wannan ra'ayoyi mabanbanta, mu a DW muke kallon yadda yakin neman zaben zai gudana a zaben da ke tafe. Jamus za ta zabi sabuwar majalisar dokoki a ranar 24 ga watan Satumban bana. A matsayinmu na kafar yada labarai ta kasa da kasa na kasar Jamus, muna son maida hankali kan abinda ke faruwa cikin kasar. Me ke sa Jamusawa gamsuwa da kasarsu bisa yanayin da ake ciki?. Me ke sa wasu na tsaron makomar rayuwar 'ya'yansu a kasar da bata tafiya bisa tsarin da suka gamsu da shi? Shin Jamus ta shirya zama kasar baki, ko kuma tsarin zaben ne wanda ya bada nasara ga masu gyamar baki da zai nuna cewa, masu zabe basa gamsuwa da inda kasar ta dosa?

Ines Pohl
Ines Pohl, babbar editar DWHoto: DW/P. Böll

Bugu da kari za mu fayyace dalilan da suka sa Jamus ta yi nasara a bangaren tattalin arziki, ya tsarin ilimin Jamus yake wanzuwa, me ya bambanta shi da na sauran kasashe. Za mu fayyace muku shugabannin siyasan kasar musamman Angela Merkel 'yar siyasa ta daban, wace ke daya a sahun fitattun mutanen duniya kuma a yanzu ta ke neman zama shugabar gwamnati a karo na hudu. Wace fata ake da ita ga 'yan siyasan kuma ina manufofin harkokin waje za su fiskanta?

Tamboyi barkatai: Yaya mahimmancin kawaye musamman kungiyar NATO? Wa ke taimakwa ci gaba wa kuma ke taimaka wa kudin ayyukan tsaro? Yaya Jamus ke kallon rawarda ta ke takawa a kungiyar Tarayyar Turai?

Tattauna da mu: Me nene Jamus?

Duk abin da muke yi muna bukatar kusanci da yin musaya tare da ku masu sauro ko karanta labarunmu ko wanda ke kallon shirinmu. bisa wannan alamar ta #askDW, wakilanmu za su aza tambayoyi su jira amsoshinku. Muna bukatar sanin abin da ku ke son fahimta, ta yaya zamu iya yi muku karin haske kuma mu bukaci ra'ayinku.

A daidai lokacin da yakin neman zabe ke karatowa, muna son koda yaushe mu kasance dandalin mahawara tare da duniya a cikin harsuna 30 da DW ke da su. Me nene Jamus? wace rawa yakamata kasar ta taka a harkokin tsaro kamar a NATO da EU? me nene fatanku ga sabuwar gwamnati da za'a zaba? Me kuke fargba? Ta wane bangare ku ke ganin Jamus ta fi karfi kuma ta ina ne rauninta? Za ku iya samun wannan alamar ta #Germaydecides. a Twitter, Facebook, TV da shafukanmu. Muna jiran muhimmiyar gwadumawarku a muhawarar. Wakilanmu a fadin duniya da editocinmu a Berlin da Bonn za su yi karin bayani, kan me ke faruwa a Jamus da kuma kan me masu zabe suka yi la'akari da shi, daga yanzu har izuwa lokacin zaben a ranar 24 ga watan Satumba.