1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan kaurar jama'a

Umar AliyuFebruary 22, 2008

Rahotan Hukumar haɗin kan tattakin arziki na OECD akan kaura

https://p.dw.com/p/DC2K
Babban Sakataren OECD Angel Gurria.Hoto: AP

Hukumar ta hadin kan tattalin arziki da raya kasashe, wato OECD tayi kira ga kasashe wakilan ta, su bada fifiko a game a matakai na kyautata zaman baki yan ci rani a kasashen su. Sakatare Janar na hukumar ta OECD, Angel Gurria ranar Laraba a Paris ya gabatar da sabon rahoton ta, game da tsarin kaurar jama'a daga kasashe masu tasowa zuwa kasashe masu ci gaban masana'antu. Da yawa daga cikin al'amura da shawarwarin da rahoton ya kunsa, suna da matukar muhimmanci da amfani yadda shike ba za'a fahimtar dalilan da suka sanya kasashen yamma basa aiwatar dasu ba.

Abin fata yanzu dai yan siyasa na kasashen hukumar ta OECD a yanzu sun bude kunnuwan su sun saurari abubuwan dake kunshe a rahoton na baya-bayan nan, saboda a hakika, rahoton abin a saurare shi ne, musmaman saboda ya kunshi cikakken bayani a game da yanayinm kaurar jama'a daga kasa zuwa kasa a karni na ashirin da daya. Rahoton ya kunshi bayanai ne da aka tara daga dukkanin kasashen hukumar ta OECD da sdakamakon kidayar jama'a daga wajejen shekara ta 2000, wadanda a karon farko aka shigar a wannan rahoto da ya zama na bai-daya. Hakan ya sanya an sami wani sakamako mai muhimmanci a game da batun kaurar jama'a da dangantakar sa da kasashe masu ci gaban masana'antu.

Abu na farko da yake tabbas shine: kasashen yamma suna bukatar yan ci rani a cikin su. Tsoffi masu yawan shekaru nan gaba sune zasu mamaye rayuwar yau da kulum a irin wadasnnan kasashe, kamar yadda aka sha ji daga sakamakon binciken game da yawan jama'a. A yunkurin ganin tattalin arzikin kasashen na yamma ba ma an kiyaye matsyin sa bane, amma har an fadada shi, ana bukatar taimako daga yan ci rani dake shiga wadnasnan kasashe. Hakan ma shi ya sanya ake samun karin kasashe dake ta kokarin jan hankalin baki yan ci rani dake da ilimi mai zurfi ko kwarewa kan fannoni dabam dabam zuwa cikin su, misali ta hanyar sassauta dokokin shiga kasashen ko koyar dasu harsuna da taimaka masu a bangaren kyautata zaman su a kasashen da suke.

Abu na biyu, wanda shima hakika yake shine: mafi yawan yan ci rani a yau, suna da ilimi ko kwarewa fiye da na yan kasashe talatin wakilan hhukumar ta OECD. A duka wadannan kasashe an gano cewar ko wane dan ci rani daya ccikin hudu yana da ilimin da yafi na yan kasar da yake zaune cikin ta.

Wani abu na ukku kuma shine mafi yawan baki yan ci rani suna aiki ne da ko kadan bai dacewa da zurfin ilimi ko kwarewar su ba. A nan Jamus alal misali, ana iya cewar kashi hamsin cikin dari na dukkanin masu tuka motocion taxi, suna da ilimin da yafi namafi yawan yan kasar. TO amma har yanzu ana ci gaba da yada zaton cewar wai baki yan ci rani suna kwacewar Jamusawa swuraren su na aiki, abin da kungiyoyi da jam'iyu na marasa kaunar baki suke amfani dashi a aiyukan su na propaganda.

Rahoton na hukumar OECD ya kuma nunar da cewar matakan kyautata zaman baki a kasashen da suke, abu ne dake iya samuwa. Rahoton na hukumarf OECD ya nunar da alamu na haske game da haka, misali a nan Jamus, inda ake bada horo na koyon harshen Jamusanci ga yayan yan ci rani, tun misalin shekara guda kafin su isa shiga makarantu.

Gaba daya idan aka duba wadannan fannoni guda hudu, ana ia cewar kasashen yamma na hukumar OECD basu koyi wani darasi daga halin da suke ciki ba. A maimakon haka, a wasu kasashen ma, akan yi amfani da batun kaurar jama'a ne domin kampe na nean kuri'un masu zabe, kamar yadda aka ghani a baya-bayan nan lokacin zaben majalisar dokokin jihar Hesse a Jamus.