1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus Akan Al'amuran Afurka

June 18, 2004

Daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na Jaridun Jamus akan al'amuran Afurka a wannan makon shi ne barazanar da ake fuskanta a game da sake billar yaki a kasar Kongo

https://p.dw.com/p/Bvpt
Mayaka da suka hada har da yara kanana a kasar Kongo
Mayaka da suka hada har da yara kanana a kasar KongoHoto: AP

A wannan makon jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyar Afurka ko da yake sun fi mayar da hankalinsu ne akan halin da ake ciki a Sudan da kuma rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar Kongo. Amma da farko zamu duba wani dogon sharhin da jaridar Financial Times ta gabatar a game da zargin da ake wa kamfanin Shell akan bannatar da kewayen dan-Adam da yake yi a Nijeriya. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"An yi shekara da shekaru kungiyoyin kare hakkin dan-Adam da kewayensa suna masu zargin kamfanin Shell a game da bannatar da kewayen yankin Delta inda yake hakan mai, amma ba ya daukar nagartattun matakai na kawar da wannan barna. Kazalika kamfanin ya ki ya cika alkawururruka da yayi na gina makarantu da wuraren kiwon lafiya ga mazauna zirin na Delta dake cikin mawuyacin hali na rayuwa. Manazarta dai sun yi wa kamfanin gargadi na cewar muddin ya ci gaba da ko oho da halin da yankin ke ciki to kuwa ko ba dade ko ba jima murnarsa zata koma ciki a game da ayyukansa a Nijeriya."

Daga Nijeriya sai mu juya zuwa Darfur ta kasar Sudan, inda jaridar mako-mako ta Rheinischer Merkur ta ce al’amura sai dada yin tsamari suke yi duk kuwa da damar da kungiyoyin taimakon jinkai suka samu na kai taimako ga jama’a. Jaridar ta ce dakarun sa kai Larabawa dake samun goyan baya daga gwamnati a birnin Khartoum su kan kai hari akan jami’an taimakon daga kasashen yammaci. Amma abin tambaya shi ne har tsawon wani lokaci ne MDD zata ci gaba da yin ko oho da wannan rikici. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Duk wanda ya bi tarihi na baya-bayan nan zai ga cewar ita gwamnatin Sudan ba ta taba ba da kai bori ya hau ba sai tare da matsin lamba, kamar dai yadda ya faru dangane da Osama Bin Ladin, wanda ta kore shi daga harabar kasar da kuma dakatar da goyan bayanta ga kungiyar Al-ka’ida sakamakon matsin kaimi na kasa da kasa. Kazalika sai tare da matsin lamba ne fadar mulki ta Khartoum ta karya alkadarin masu fataucin bayi da kuma dakatar da hare-haren jiragen saman yakinta a kudancin Sudan. Ta la’akari da haka tilas ne duniya ta tashi tsaye saboda a wannan marra da muke ciki yanzu babu wani alamar dake yin nuni ga kawo karshen ta’asar dake wanzuwa a Darfur nan ba da dadewa ba."

A can kasar Kongo ma ana zargin MDD da rashin tabuka kome domin dakatar da kisan gillar da ake wa farar fula da kuma kandagarkin billar wani sabon fada a kasar, wacce rikicinta ya ki ci ya ki cinyewa. A lokacin da take sharhi game da halin da ake ciki a gabacin Kongo mujallar Der Spiegel cewa tayi:

"Abin mamaki shi ne yadda kasashen Turai ke kalubalantar shugaba Robert Mugabe a game da manufofinsa na kama karya, a yayinda Kagame yake da ikon cin karensa ba babbaka. Domin kuwa daga baya-bayan nan Ruwanda ta sha barazanar sake tura sojojinta zuwa kasar Kongo. Dalili kuwa shi ne kasancewar tana daya daga cikin kasashen dake cin gajiyar mawuyacin hali na zaman dardar da ake ciki a Kongo. Kuma ko da yake dakarun ‘yan tawayen da take ba su goyan baya sun janye daga Bukavu, amma farmakin da suka kai abu ne da ya sake jefa kasar Kongo bakin dayanta cikin wani hali na rashin sanin tabbas a game da makomar zaman lafiyarta."

A cikin wata sabuwa kuma wakilin MDD dake shiga tsakani domin sasanta rikicin yammacin Sahara, James Baker, ya kakkabe hannuwansa daga wannan manufa saboda takaicin rashin samun hadin kai daga kasar Moroko dake mamayar yankin na yammacin Sahara. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ba da rahoto game da haka tana mai cewar:

"A makon da ya gabata ne James Baker, wanda aka ce ya amsa kiran da shugaba Bush yayi masa domin taimaka masa a yakin neman zabe, ya ba da sanarwar janyewa daga manzanci na musamman da MDD da dora masa a fafutukar sasanta rikicin yankin yammacin Sahara, wanda aka yi kusan shekaru talatin ana fama da shi, sakamakon mamayar da Moroko ke wa yankin. A yayinda kungiyar Polisario da kawarta Aljeriya suka amince da shawarar da Baker ya bayar, fadar mulki ta Rabat ta sa kafa tayi fatali da wannan shawara."

To masu sauraro da wannan muke kammala sharhin jaridun na Jamus akan al’amuran Afurka, sai kuma in ce Mani gare-ka.