1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka daga 16 zuwa 20 ga watan agusta

Mohammad Nasiru AwalAugust 20, 2004
https://p.dw.com/p/Bvpm

Madalla, jama´a barkanku da warhaka. A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan kasar Burundi, bayan kisan gillan da aka yiwa ´yan gudun hijirar Banyamulenge na kabilar Tutsin kasar Kongo kimanin 160 a wani sansanin ´yan gudun hijirar MDD dake Gatumba a cikin yankin kasar Burundi. A cikin sharhin da ta rubuta jaridar TAZ ta rawaito jami´an MDD a Burundi na nuna fargabar sake barkewar rikici a Burundi. Bayan da ´yan tawayen Hutu suka yi ikirarin aikata wannan danya, MDD ta dakatar da kokarin yin sulhu da take yi tsakanin ´yan tawayen kungiyar FNL da gwamnatin Burundi har sai abin da hali yayi. Kungiyar FNL ce kadai ba ta sanya hannu akan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a Burundi ba. Yanzu haka dai wani taron kolin kungiyar kasashen Afirka a Tanzania ya saka sunan kungiyar ´yan tawayen a jerin kungiyoyin ´yan ta´adda. Taron ya jaddada cewar babu ja da baya a shirye-shiryen gudanar da zabe a Burundi a karshen watan oktoba. To sai dai jaridar ta ce a dangane da halin rashin sanin tabbas, da wuya a iya gudanar da zaben a wannan lokaci.

Ita kuwa jaridar FAZ cewa ta yi dole kasashen Burundi da Rwanda su sa kafar wando guda da ´yan kabilar Hutu masu matsanancin ra´ayi. Jaridar ta rawaito hukumomin kasashen biyu na yiwa kasar Kongo hannun ka mai sanda, inda suka zarge ta da taimakawa ´yan tawayen Hutu, wadanda ke yiwa kokarin wanzar da zaman lafiya a Burundi zagon kasa.

A wani rahoton na daban, har wayau jaridar FAZ ta labarto mana cewar sakatare-janar na MDD Kofi Annan yayi kira da a kara yawan sojojin wanzar da zaman lafiya majalisar a Kongo, daga dubu 10 da 800 zuwa dubu 23 900 don tabbatar da gudanar da zaben wannan kasa cikin lumana a badi idan Allah Ya kaimu.

A dangane da kasar Sudan kuwa jaridar cewa ta yi kwararar ´yan gudun hijirar yankin Darfur na jefa kasar Chadi cikin wani mawuyacin hali. Yanzu haka akwai ´yan gudun hijirar Darfur fiye da dubu 180 a wani yanki da zai iya daukar ´yan gudun hijira dubu 80 kadai. Hakan dai wani babban nauyi ne ga Chadi, wadda ita kanta take fama da matsalolin tattalin arziki. Ita ma jaridar TAZ ta labarto mana wannan hali da aka shiga a Chadi sakamakon kwararar ´yan gudun hijirar Darfur, wadanda ke tserewa rikicin da yaki ci yaki cinyewa a wannan yanki dake yammacin Sudan. A farkon wannan mako ´yan gudun hijira fiye da 500 ne suka tsallaka zuwa Chadi.

Ita kuwa jaridar FR ta mayar da hankali ne akan mawuyacin halin da kananan yara fiye da miliyan daya suke ciki a arewacin Uganda, sakamakon ta´asar da sojojin ´yan tawaye karkashin jagorancin Joseph Kony ke aikatawa. Jaridar ta ce a cikin shekaru biyun da suka wuce ´yan tawayen sun saci yara maza da mata kimanin dubu 12, inda suke tilasta musu shiga aikin soja. Jaridar ta rawaito asusun taimakon kananan yara na MDD, UNICEF na cewa a kowace ranar Allah Ta-alah yara kimanin dubu 60 ke tserewa daga kauyukansu na asali zuwa garuruwan dake kusa. Saboda haka asusun yayi kira da a dauki sahihan matakan kare lafiyar wadannan yara. A wani rahoton da ta buga har wayau jaridar ta FR ta rawaito ministar raya kasashe masu tasowa ta tarayyar Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul na yin kira ga kasashe masu arziki da su kara yawan jarin da suke zubawa a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce ko da yake ana sa ran samun karin kudaden shiga sakamakon tashin farashin man fetir da zinariya da kuma auduga a kasuwannin duniya, amma hakan ba zai samar da wani abin a zo a gani ba ga nahiyar Afirka. Saboda haka ya zama wajibi kasashe masu arziki su kara kawad da shigayen da suke sanyawa a huldodin cinikinsu da kasashen Afirka.

To Allah Ya kyauta. Jama´a yau kuma a nan zamu dakata a shirin na Afirka A Jaridun Jamus.