1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru AwalDecember 10, 2004

Rikicin yankin gabashin Kongo da ake yi da Rwanda na daga cikin muhimman batutuwan da jaridun Jamus suka mayar da hankali kai a wannan mako.

https://p.dw.com/p/Bvpb

Jama´a barkanku da warhaka. To a cikin wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan kasar Rwanda, wadda ta tura dakarun zuwa gabashin JDK, sai rangadi kwanaki 10 da shugaban Jamus Horst Köhler yake kaiwa nahiyar Afirka.

A cikin wani rahoto da ta buga jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito majiyoyin kwamitin sulhu na MDD na yin kira ga Rwanda da ta ta kawo karshen matakan sojin da ta ke dauka a yankin gabashin kasar JDK. Jaridar ta rawaito shugaban kwamitin sulhu a yanzu wato Abdallah Baali dan kasar Tunisia na cewar sun samu rahotanni masu tushe dake tabbatar da kasancewar sojojin Rwanda a yankin makwabciyarta wato Kongo, wanda hakan ya sabawa kudurorin MDD da kuma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar wannan yanki da aka kulla.

Ita ma a nata sharhin jaridar Tageszeitung ta rawaito kwamitin sulhu na MDD na yin Allah wadai da wannan mataki da Rwanda ta dauka, da cewa babbar barazana ce ga shirin wanzar da zaman lafiyar yankin ga baki daya. Saboda haka gamaiyar kasa da kasa ta yi kira ga Rwanda din da ta hanzarta janye dakarunta, ko kuma a ja kunnen ta. Jaridar ta ci-gaba da cewar yanzu dai kimanin makonni biyu kenan da Rwanda din ta yi barazanar tura sojojin ta wannan yanki don su fatattaki ´yan tawayen kabilar Hutu, to amma har yanzu tana musanta cewar sojojin ta sun kutsa cikin Kongo.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau ta rubuta sharhi akan zaben shugaban kasa da na ´yan majalisar dokokin kasar Ghana, wadda ta bayyana ta da cewa tun bayan kawo karshen mulkin shugaba Jerry Rawlings a cikin shekara ta 2000 ta kasance zakaran gwajin dafin wanzuwar mulkin demukiradiyya a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce ganin yadda zabukan da ake yi a kasar ta Ghana ke gudana cikin kwanciyar hankali da lumana tare da zaman lafiyar da kuma kyakyawan yanayin siyasa, yanzu haka kasar ta zama abar koyi ga sauran kasashen yankin yammacin Afirka. A ma halin da ake ciki kasar ta zama dandalin tarukan samar da zaman lafiya a makwabtanmta wato Kodivuwa da kuma Liberia. Jaridar ta kara da cewa duk da dan ci-gaba da gwamnatin Kufour ta samu wajen ta da komadar tattalin arzikin kasar, amma hakan ya fi yin tasiri ne a babban birnin kasar wato Accra, yayin da a sauran yankunan kasar musamman a arewaci, akasarin mutane ke zaune cikin matsanancin talauci. Jaridar ta taya shugaba Kufour murnar sake lashe zaben sannan ta yi masa fatan alheri a matakan da yake dauka na asamarwa al´umar kasarsa wata makoma ta gari.

Har yanzu dai muna yankin yammacin Afirka, inda a farkon wannan mko shugaba tarayyar Jamus Horst Köhler ya fara rangadin kwanaki 10 da yake kawai nahiyar Afirak. A cikin sharhin da ta rubuta jaridar TAZ ta yabawa kalaman da shugaban yayi cewar zai yi amfani da wannan ziyara don jawo hankalin duniya ga nahiyar Afirka. Yanzu haka dai shugaba Köhler ya isa janhuriyar Benin, bayan ya ziyarci kasar Saliyo, inda yayi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta kara wa´adin aikin da take yi na wanzar da zaman lafiya a Saliyo. A ran lahadi shugaban na tarayyar Jamus zai zarce zuwa kasar Habasha sannan a ran alhamis mai zuwa ya karasa zuwa Jibuti, inda zai ziyarci sojojin Jamus da aka girke a yankin tekun Bahar Maliya a karkashin aikin yaki da ta´addanci na kasa da kasa.