1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus game da Afirka

Sadissou YahouzaSeptember 4, 2009

Jaridun Jamus sun yi sharhuna masu yawa agame da ƙasashen Afrika wanda suka haɗa da Najeriya, Mali ,da Kongo.

https://p.dw.com/p/JSXJ
Afirka a Jaridun JamusHoto: dpa

A halin da ake ciki yanzu fataucin mata tuni ya fi samar da riba akan safarar miyagun ƙwayoyi da cinikin makamai. Wannan shi ne ra'ayin da jaridar Süddeutsche Zeitung ke ɗauke da shi a cikin wani rahoton da ta rubuta dangane da wannan matsala. Jaridar ta ce:

Kimanin mata dubu 40 daga Nijeriya ake tilasta su aikin karuwanci a sassa na Turai. Tun a cikin shekarun 1970 ne aka samu kafuwar ƙungiyoyin fatauci da barandar karuwai a garin Benin na Nijeriya. Yawancin masu hannu a wannan ciniki mata ne da aka taɓa tilasta su aikin karuwanci, waɗanda suka gama biyan bashin dake kansu kuma a yanzu suke haɗa kan hada-hadar ƙarƙashin taken: "Magajiya". Dangane da waɗanda suka kasa biyan basussukan kuwa akan yi musu barazana da matakai na tsafi ko kisan kai.

Duk da cewar sojojin gwamnati a janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo sun samu gagarumar nasara a matakin kutsen da suka ɗauka baya-bayan nan akan 'yan tawayen Hutun Ruwanda dake ƙarƙashin ƙungiyar FDLR, amma fa babu wata alamar dake nuna kyautatuwar rayuwar jama'a a yankunan dake ƙarƙashin ikon sojojin na gwamnati, in ji jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce:

A maimakon haka sojojin sai ƙwace da kuma fyaɗe suke yi ba ji ba gani. Bugu da ƙari kuma manazarta na yankin sun nuna cewar dakarun ƙungiyar ta FDLR su kan ja da baya ne domin su sake sabon yunƙurin ƙwace yankunan a cikin hamzari. A baya ga haka a maƙobciyar ƙasa ta Burundi ana fafutukar haɗa kan wasu sabbin 'yan tawayen Hutu. Har dai ya zuwa watan yulin da ya wuce an ƙiyasce yawan mutanen da aka fatattaka sakamakon yaƙin ya zarce mutum dubu ɗari shida.

Ƙasar Mali dai ita ce ta uku a jerin ƙasashen da suka fi talauci a duniya. A sakamakon rashin aikin yi ko rashin albashi mai tsoka da yawa daga matasa na ƙasar kan yi ƙoƙarin shigowa Turai ba a bisa ƙa'ida ba bisa fatan samun aiki da kuma tallafa wa danginsu. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Handelsblatt cewa tayi:

Tun shekarar da ta wuce ƙungiyar tarayyar Turai ta buɗe cibiyar ilimantarwa da bayanai don shawo kan matsalar guje-gujen hijira a ƙoƙarin janyo hankalin matasan na Mali akan haɗarin dake tattare da matsalar. To sai dai kuma kawo yanzu wasu 'yan Mali 'yan ƙalilan ne suka samu shiga ƙasar Spain a maimakon ɗaruruwan da aka shirya tun farko domin kama aiki; kamar dai Abdoulaye Doumbia, wanda ya samu aikin amma aka hana masa bisa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohamed Nasiru Awal