1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Larabawa akan rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya

July 18, 2006

Masharhanta na jaridun Larabawa sun bayyana ra'ayoyi iri daban-daban dangane da rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/BvPm

A cikin wani sharhi da ta gabatar jaridar Arraya ta gwamnatin kasar Qatar dake fita kullu-yaumin tayi gargadi a game da ire-iren abubuwan da zasu biyo bayan hare-haren Isra’ila akan kasar Lebanon tana kuma mai ba da la’akari da fursinoni Larabawa dake tsare a gidajen kurkukun Isra’ila. Jaridar ta ce:

“Isra’ila har yau tana ci gaba da yin ko oho da kaddarar dake kanta, wadda ainifi ita ce ginshikin rikici tsakaninta da Larabawa. Matakan hare-hare da sojan Isra’ilar ke dauka ba zai tsinana kome ba illa ya kara sarkakewar al’amuran yankin da rikicinsa ya ki ci ya ki cinyewa. Garkuwar da ake yi da sojan Isra’ilar wata manufa ce ta gwagwarmayar al’umar Lebanon domin ganin an saki dukkan fursinonin dake tsare kuma a saboda haka Isra’ila ba ta da zabi illa ta amince da musayar fursinonin.”

Ita kuwa jaridar Assafir ta kasar Lebanon dake da matsakaicin ra’ayin gurguzu cewa tayi:

“Isra’ila ta sake komawa ga matakan nuna karfin bindiga akan makobciyarta mai rauni. Kasar ka iya lalata hanyoyin sadarwa a Palasdinu da Lebanon, ta kashe shuagabannin kungiyoyin Hamas da Hizbullah, watakila ma ta kai farmaki kan Siriya da Iran, amma fa wajibi ne da zan da sanin cewar hakan ba zai taimaka a shawo kan rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya ba. Isra’ila ta kasa hangen nesa tana mai amfani da takaitaccen sabanin da ke fuskanta da kuma matsaloli na cikin gidan Palasdinawa, kuma irin wannan yunkurin ne take kokarin yi a Lebanon yanzu haka. Amma faufau Isra’ila ba zata cimma biyan bukata ba. Al’umar Lebanon har abada ba zasu mika wuya ba. Ba zasu ba da kai bori ya hau ba.”

A nata bangaren jaridar Assark Al-Awsat ta kasar saudiyya tayi bayani ne akan rawar da shugaban Ahmadinajad na kasar Iran ke takawa a wannan rikici, inda ta ce:

“Ahmadinajad ya gargadi Isra’ila da cewar akul ta kai farmaki kan Siriya. Ya ce in har Isra’ilar tayi haka to kuwa ta keta haddin jan zirin da aka shata. Amma wadannan lafuzza suna da ban mamaki. Domin kuwa abin tambaya shi ne me ya hana kasar ta Iran yin katsalandan dangane da farmakin da Isra’ila take kaiwa kudancin Lebanon shelkwatar kungiyar Hizbullah kuma ba tayi batu a game da keta jan zirin dake akwai ba. Ga alamu dai so take ta sadaukar da ran kungiyar Hizbullah.”

Daga can kasar Siriya kuwa jaridar Athawra cewa tayi:

“Isra’ila babbar makaryaciya ce inda take ikirarin cewar ta gabatar da wannan yakin ne domin kare kanta daga ta’asar Hizbullah ko kuma don ta kwato sojojinta da ake garkuwa da su. Akwai dalilai da dama game da wannan yaki da Isra’ila ta gabatar. Babbar manufar ta kuwa shi ne shan fansa akan Lebanon, musamman ma a game da yadda ta kwashi kashinta a hannu kafin ta janye daga kudancin Lebanon shekaru shida da suka wuce.”

A nata bangaren jaridar Alahram ta kasar Masar cewa tayi a takaice:

Wannan yaki tsakanin Isra’ila da da kungiyar Hizbullah an gabatar da shi ne ba tare da lissafi ko hangen nesa ba. Ga alamu kungiyar na sane da abin da zai biyo baya idan tayi garkuwa da sojan Isra’ila. Ita kuwa Isra’ilar a nata bangaren a baya ga kokarin kwace sojojinta, kazalika tana da nufin karya angizon da Hizbullah ke da shi ne a wannan yanki. Dangane da Iran dake mara wa Hizbullah kuwa wajibi ne a gane cewar a yanzu tana da wani kakkarfan matsayi na siyasa da soja a shiyyar gabas ta tsakiya.