1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhohin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka.

YAHAYA AHMEDOctober 28, 2005

A wannan makon, jaridun Jamus sun yi sharhohi da dama a kan nahiyar Afirka, inda suka takalo batutuwan da suka shafi halin siyasa, da na tattalin arziki da na zaman jama’a a kasashen nahiyar. Amma galibin jaridun sun fi mai da hankullansu ne kan halin da ake ciki yanzu a kasar Côte d’Ivoire, inda wa’adin shugaban kasar Laurent Gbagbo zai cika a ran 30 ga wannan watan na Oktoba. To ko yaya za a ci gaba da tafiyad da harkokin siyasa kasar daga nan ?

https://p.dw.com/p/BvQH
Jaridar die tageszeitung
Jaridar die tageszeitungHoto: npb

A kan wannan tambayar ne jaridar die Tageszeitung ta yi sharhinta, inda ta ari bakin shugaban jaridar nan ta Nord-Sud ta birnin Abidjan, Moussa Traoré, yana mai cewar, zai rufe ofisoshin ma’aikatarsa saboda riga kafin abin da zai iya aukuwa bayan ran 30 ga wata. A zaihiri dai, inji jaridar die Tageszeitung, ko yauashe wani rikici ya karke a birnin na Abidjan, jaridu masu sukar lamirin gwamnati ne ake fara kai musu farmaki. A halin da ake ciki, mazauna birinin ma sun fara daukan matakan kare kansu idan rikici ya karke. Kowa na koakarin sayen kayayyakin masarufi ne da zai ajiye a gidansa, inda zai sami abin ciyad da iyalansa ko da ta kaci. Sabili da haka, rahotanni na nuna cewa, a halin yanzu silindan hayakin gas na girki sun yi karanci a birnin. Tuni dai shugaba Gbagbo ya yi wani taron gaggawa da shugabannin rukunan soji da na wasu kafofin tsaron kasar, don tsara matakan da za a dauka a birnin na Abidjan idan rikici ya karke.

Jaridar ta kara da cewa, bisa kudurin da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya zartar dai, shugaba Gbagbon zai zarce da mulki bayan cikar wa’adinsa, har zuwa tsawon wani lokaci, wanda ba zai wuce shekara daya ba. A cikin wannan lokacin ne za a shirya zake. To sai dai, kwamitin ya kuma bukaci shugaban ya nada Firaiminista. Amma abin da ake korafi a kansa yanzu shi ne wanda zai rike wannan mukamin na Firamiya.

A karshe dai, die Tageszeitung, ta bayyana ra’ayin cewa karkewar rikici a kasar ko kuma zaman lafiya, zai dogara ne kan yadda jam’iyyun adawa za su tinkari wannan batun. Wai shin za su yi shiru ne su sa ido su ga irin rawar da shugaba Gbagbon zai taka, bayan cikar wa’adinsa, ko kuwa za su yi kokarin kwace mulkin ne tun daga ran litinin mai zuwa ?

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ita ma ta yi sharhi a kan rikicin na kasar Côte d’Ivoire, inda ta ce tun shekaru 3 ke nan a jere da ake ta gwabza yakin basassa a wannan kasar ta Afirka ta Yamma. Duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cim ma, inda aka kafa gwamnatin wucin gadi da ta kunshi kangarorin gwamnatin shugaba Gbagbo da na kungiyoyin adawa, da girke dakarun kare zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya dubu 10 a kasar da kuma wani rukuni na musamman da ya kunshi dakaru dubu 4 na sojin Faransa, har ila yau dai ba a cim ma kusantar juna tsakanin kangarorin ba. A daura da haka ma, babu kangaren da ke kiyaye ka’idojin yarjejeniyoyin da aka cim ma, tun dag ta Marcoussis, da ta birnin Lomé zuwa ta Accra da kuma birnin Pretoria.

Game da takarkarewar al’amura a kasar ne dai, gamayyar kasa da kasa ta tsai da shawarar dage lokacin zaken kasar a ran 30 ga wannan watan, har zuwa wani lokaci nan gaba, inda kuma aka tsawaita wa’adin mulkin shugaba Gbagbo har tsawon watanni 12.

Jaridar Handelsblatt ta yi sharhi ne kan yarjejeniyar da Najeriya ta cim ma da kasashen da ke binta bashi, inda suka amince su yafe mata kashi 60 cikin dari na basussukanta. Rukunin nan na Paris Club, wanda ya kunshi kasashen da ke bin Najeriya bashin, ya amince da yarjejeniyar ne don mara wa Najeriyan baya a yunkurin da take yi na aiwatad da wasu canje-canje a fannin tattalin arzikinta da kuma taimakawa wajen yin rigakafin karkewar rikice-rikice a yankin.

A halin yanzu dai, Najeriya, bisa yarjejeniyar da aka cim ma a karshen makon da ya gabata, inji jaridar, za ta biya dola biliyan 6 da digo 5 ga rukunin na Paris Club. Rukunin kuma ya amince ya yafe wa Najeriyan dola biliyan 18 daga jimlar kimanin dola biliyan 30 da ake binta. Jaridar ta kara da cewa, kasashe 19 na rukunin sun yabi irin matakan da shugaba Olusegun Obasanjo ke dauka na yi wa kafofin tattalin arzikin kasar garambawul, da kuma na yakan cin hanci da rashawa. Sai dai, bisa wani rahoton da kungiyar ta Transparency International ta buga, har ila yau illar cin hanci da rashawa ta kankama sosai a Najeriyan.