1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhuna akan kasashen Afrika

Ahmad Tijani LawalJanuary 7, 2008

Jaridun Jamus sunyi tsokaci dangane da halin siyasar da Kenya ke ciki

https://p.dw.com/p/Clad
Masu gangami a KenyaHoto: AP

A wannan makon ma, daidai da makonni biyun da suka gabata, halin da ake ciki a ƙasar Kenya, musamman ma tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 27 ga watan disamba, shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus. A cikin wani sharhin da ta gabatar jaridar Kölner Stadt-Anzeiger cewa tayi:

“Ƙasar Kenya na cikin mawuyacin hali na tashe-tashen hankula sakamakon saɓani tsakanin shugaba mai ci Mwai Kibaki da abokin hamayyarsa Raila Odinga dangane da zaɓen kasar, wanda Odinga ke tattare da imanin cewar an tafka maguɗi a cikinsa. A yayinda shugaba Kibaki ke fafutukar nuna ƙarfin iko na mulki, shi kuma Odinga a nasa ɓangaren ƙoƙari yake yi ya nuna wa shugaban cewar ya fi shi goyan baya. Muddin abokan gabar guda biyu ba su nuna halin sanin ya kamata suka ɗinke wannan ɓaraka dake tsakaninsu ba, da wuya ƙura ta lafa a wannan rikici mai kama da yaƙin basasa.”

Ita kuwa jaridar kasuwanci ta Handelsblatt a cikin nata sharhin da ta gabatar ƙarƙashin taken: “Mulki da ƙarfin kulake da barkonon tsofuwa”, cewa tayi:

“Wani abin lura a game da sakamakon zaɓen ƙasar Kenya shi ne amfani da ƙarfin hatsi da jami’an tsaro na shugaba Kibaki suke yi akan masu zanga-zangar adawa dake neman ganin an tsage gaskiya. ‘Yan sanda na amfani da kulake da barkonon tsifuwa da motoci masu feshin ruwan zafi akan matasa dake zanga-zanga daure da fararen ƙyale a kawunansu suna masu rera taken ƙasar domin zama wata alama ta zanga-zangar lumana. Dubban-dubatar al’umar Kenya suka kama hanyar gudun hi9jira domin neman mafaka a ƙasashe maƙobta, lamarin dake nuna irin mummunan tasirin da wannan rikicin zai yi akan waɗannan ƙasashe muddin ba a kawo ƙarshensa a cikin hamzari ba.”

Amma jaridar Süddeutsche Zeitung ɗora laifin wannan ci gaba tayi akan ƙasashe na ƙetare, musamman ma na yammaci kamar Amurka da Ƙungiyar Tarayyar Turai, inda take cewar:

“Duk wanda yayi bitar ci gaba na baya-bayan nan zai tabbatar da cewar kafofi na ƙasa-da-ƙasa sun yi ko in kula da ainifin abin dake faruwa a ƙasar Kenya a zahiri. Domin kuwa dukkan jami’an siyasar ƙasashen Turai da Amurka da kan kai ziyara ƙasar su kan yaba mata da kasancewa kasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban demoƙraɗiyya. Amma fa a haƙiƙa tun ba yau ba ake hangen wata alamar dake nuna cewar al’amura zasu iya canzawa su ɗauki wani sabon salo a cikin ƙiftawa da Bisimilla.”

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung tana hangen taɓarɓarewar al’amuran tsaro ne sakamakon wannan mawuyacin hali, inda take cewar:

“An sha fuskantar tashe-tashen hankula da saɓani na ƙabilanci a ƙasar Kenya, amma fa martanin da al’umar ƙasar ke mayarwa sakamakon zaɓen da aka gudanar a yanzun wani lamari ne na dabam. Domin kuwa yadda wasu ƙabilun ƙasar ke tace mutane akan hanya domin yi musu kisan gilla saboda sun zama ‘ya’yan wata ƙabila dabam, ba alheri ba ne ga makomar ƙasar ta gabacin Afurka, saboda a ƙasar Ruwanda ma da haka aka fara kafin lamarin da yaki ga kisan kiyashin da ya wakana a shekara ta 1994. Duk dai wanda ya samu galaba a rikicin siyasar da ƙasar ke fama da shi yanzun wajibi ne ya ɗauki nagartattun matakai na kare lafiyar illahirin al’umarta ba tare da la’akari da ƙabilanci ba.”

Ita ma jaridar nan ta Financial Times Deutschland ta tofa albarkacin bakinta inda take cewar:

“Ƙasar Kenya wadda a zamanin baya ta zama tamkar wani dausayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali, a yanzun ta shiga wani hali mai kama da gigin barci. A misalin shekaru biyar da suka wuce jama’a sun ba da cikakken goyan baya ga Mwai Kibaki domin kakkaɓe dan kama karya Daniel arap Moi daga karagar mulki, amma a yanzun sa ga shi yana neman tabbatar da madafun iko a hannunsa ko ta halin ƙaƙa ba tare da la’akari da asarar rayuka ba.”