1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridu

Lawal, TijaniMarch 30, 2008

Afurka a Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/DXSL
Shugaba Robert Mugabe, yana kaɗa kuri'ar sa.Hoto: AP


Zimbabwe/Kongo/Somalia

Halin da ake ciki a kasar Zimbabwe dangane da zaɓen kasar na ranar asabar shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus a wannan makon. A cikin nata sharhin jaridar Die Zeit nuni da tyi da cewar.


"Ba wani mai tababa a game da cewar shugaba Mugabe ne za a ayyuna a matsayin mai nasarar zaben Zimbabwe. Shugaban na fatan yin mulki ne na rai-da-rai. Babban abin mamaki game da Mugabe shi ne yadda gaba daya ya rikide daga jigon fafutukar famar neman 'yancin kai zuwa dan kama-karya. A yayinda a zamanin baya ake yabawa da irin rawar da ya taka wajen samarwa da kasarsa 'yancin kanta tare da dawo wa al'umarta daraja da martabarsu da kuma dinke barakar dake akwai tsakaninsu da farar fata, a yanzun bayan shekaru 28 na mulki, Mugabe ya wayi gari tamkar abin tsoro da kyama a kasar Zimbabwe."

Zimbabwe

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tayi nuni ne da yadda rayuwa ke dada tsada a kasar Zimbabwe da kuma fatan dake tattare a zukatan al'umar kasar na samun wani shugaban da zai aiwatar da garambawul, wa la'alla su samu sararawar lamarin. Jaridar ta ce:


"A inda take kasa tana dabo shi ne, muddin Mugabe bai cimma rinjaye na akalla kashi 50% a cikin kwanaki uku da za a yi ana kidayar kuri'un ba, to kuwa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin an canza alkaluman saboda ba zai so ya shiga wani sabon zabe na fid da gwani makonni uku nan gaba ba."

Kongo

A wata sabuwar tabargazar da aka fallasa a wannan makon kuma, binciken da aka gudanar a kasar Sweden ya zargi sojojin Faransa da laifukan azabtar da fursinoni lokacin da kungiyar tarayyar Turai ta tura sojojinta zuwa Bunia ta kasar Kongo a shekara ta 2003. Jaridar Die Tagezeitung dake ba da wannan rahoton ta ce:


"Wani bincike na wani shirin gidan telebijin a kasar Sweden mai suna "Uppdrag Granskning" shi ne ya fasa kwai. Kuma jim kadan bayan gabatar da shirin mahukuntan sojan kasar suka ba da wata sanarwar dake tabbatar da wannan tabargaza ta azabtar da fursinoni da sojan Faransa suka rika yi a karkashin matakin da aka kira wai "Operation Artemis", wanda aka rika yaba masa da kasancewa abin koyi dangane da aikin sojan kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afurka."

Somaliya

A ƙasar Somaliya akwai barazanar sake faɗawa cikin mawuyacin hali sakamakon kazamar fafatawar da ake yi da dakarun kungiyoyin musulmi na kasar, abin da ya kai kungiyar taimakon yara ta MDD UNICEF ga cewar ba inda kananan yara ke fama da mawuyacin hali na ruyuwa a wannan duniya ta mu kamar a kasar Somaliya. Tuni kungiyoyin taimako 40 dake gudanar da ayyukansu a Somaliyar suka yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya gudanar da wani zama na gangami domin bitar halin da Somaliyar ta samu kanta a ciki, in ji jaridar Die Tageszeitung, wadda ta kara da cewar:

"Sama da mutane miliyan daya 'yan kasar Somaliya suka tagayyara, kuma a kullu-yaumin adadin sai kara yawa yake yi sakamakon sabon fadan da ya sake barkewa tsakanin dakarun kungiyoyin musulmi da sojan Somaliya dake samun rufa baya daga asakarawan Habasha."

.