1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridu

Zainab MohammedFebruary 16, 2009

Sharhunan Jaridun Jamus akan Afrika

https://p.dw.com/p/GvQ8
Hoto: AP

Zimbabwe/Madagaska/Mali

A wannan makon mai karewa dai ci gaban da aka samu a kasar zimbabwe, inda aka nada Morgan tsvangirai sabon P/M a kasar mai fama da rikici, shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da nahiyar ta Afurka. A cikin nata sharhin jaridar Die Tageszeitung cewa tayi a takaice:

"A yanzun an karya alkadarin shugaba Robert Mugabe dangane da kane-kane da yayi a al'amuran mulkin Zimbabwe. Shi kansa shugaban ne ya rantsar da sabon P/M kuma babban dan hamayya Morgan Tsvangirai akan wannan mukami, ko da yake ba a biya masa dukkan bukatunsa ba. Babban aikin dake gaban sabuwar gwamnatin dai a yanzu shi ne ta tada komadar tattalin arzikin kasar da ya tabarbare kwata-kwata."

Marc Ravalomanana Staatspräsident Madagaskar
Marc RavalomananaHoto: picture-alliance/ dpa

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiel ra'ayi ta nuna cewar da wuya wannan auren tilas tsakanin Mugabe da Tsvangirai ya dore. Domin kuwa ba irin yunkurin da masu tsattsauran ra'ayi a jam'iyyar ZANU-PF ta shugaba Mugabe ba su yi ba wajen hana ruwa gudu ga tabbatuwar wata gwamnati ta hadin kan kasa, wadda kungiyar hadin kan tattalin arzikin kudancin Afurka ta tilasta kan sassan biyu da basa ga maciji da juna.

A can tsuburin Madagaskar dake makobtaka da Afurka ta Kudu a yankin kudu maso gabacin Afurka har yau ana ci gaba da fama da tashintashinar siyasa, wadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta kira:"Gwagwarmayar kama madafun iko tsakanin wasu hamshakan 'yan kasuwa guda biyu". Jaridar ta ci gaba da cewa:

Chinas Präsident Hu Jintao mit König Abdullah bei seiner Ankunft in Saudi Arabien
Sarki Abdullah da Hu JintaoHoto: AP


"Andry Rajoelina na gwagwarmayar kama madafun iko ne ko ta halin kaka. Kuma abin dake faruwa a yanzun ya kusa yayi daidai da irin abubuwan da suka wakana a zamanin baya ya zuwa shekara ta 2001 lokacin da aka zabi Ravalomanana sabon shugaba domin ya maye gurbin tsofon shugaba Ratsiraka. Ya zuwa wancan lokaci shi kansa Ravalomanana yana rike ne da mukamin magajin garin Antananarivo. Ta la'akari da ire-iren abin dake faruwa yanzun, bai zama abin mamaki ba kasancewar da yawa na kyautata zaton cewar Ratsiraka ne ke iza keyar Rajoelina don ta da zaune tsaye a kasar da aka santa da zaman lafiya a zamanin baya."

A wannan makon shugaban kasar China Hu Jintao ya fara ziyarar mako daya ga kasashen Afurka dake kudu da hamadar sahara, inda yake bukatar nuna wa kasashen na Afurka cewar China wata amintacciyar kawa ce da zasu iya dogara da ita a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Wannan dai shi ne karo na hudu da shugaban na China ke ziyarar Afurka, yana kuma samun karbuwa da hannu biyu-biyu musamman ma a kasashen dake fama da gibin demokradiyya kuma a saboda haka suke neman abokan hulda, wadanda ba su gindaya wasu sharudda na siyasa."