1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus akan Nahiyar Afrika

February 16, 2010

Shekaru 20 da sakin Nelson Mandela, bayan ɗauri na kusan shekaru talatin a gidan yari

https://p.dw.com/p/M3Dg
Jaridun JamusHoto: DW

Ko da yake jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka, amma sun fi mayar da hankali ne kan wasu abubuwa guda biyu. Da farko a game da samun shekaru 20 da sakin Nelson Mandela, bayan ɗauri na kusan shekaru talatin, inda daga bisani kuma ya shugabancin ƙasar Afirka ta Kudu. A cikin nata rahoton jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

"A wajejen maraicen ranar 11 ga watan fabarairun shekara ta 1990 ne fursuna Nelson Mandela ya bayyana gaban jama'a bayan da aka sake shi daga gidan kurkuku. Sai kuma bayan da ya tsaya gaban dubban ɗaruruwan jama'ar da suka hallara domin su taya shi murna ne ya lura cewar ya manta da tabaransa a can gidan kurkukun. A jawabin da yayi wa jama'a dai ya buɗe ne da sunan zaman lafiya da demoƙraɗiyya da walwala. Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi tsawon shekaru huɗu Mandela ya jagoranci ƙungiyar ANC zuwa ga lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya zama baƙar fata na farko da shugabanci ATK. To sai dai abin takaici shi ne bayan kakkaɓe hannuwansa daga al'amuran mulki murna ta sake komawa ciki dangane da haɗin kan al'umar Afirka ta Kudu."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

Rezensionsbild - Nelson Mandela -<br>Ein Leben für Frieden und Freiheit
Nelson MandelaHoto: IMPORT

"Har yau tsofon shugaban farko a tsarin demokraɗiyya tsantsa na Afirka ta Kudu Nelson Mandela yana zama abin misali ga manufofi na da'a da halin sanin ya kamata. Duk da cewar yayi ritaya amma akai-akai tsofon shugaban mai kwarjini ya kan tofa albarkacin bakinsa domin ya tunasar da jami'an siyasar Afirka ta Kudu akan ɗabi'ar sanin ya kamata da rungumar alhakin dake kansu da hannu biyu-biyu da kuma ƙara neman kusantar juna tsakanin illahirin jinsunan munaen da Afirka ta Kudu ta ƙunsa."

A tsakiyar wannan makon ba zato ba tsammani majalisun dokoki da na dattawan Nijeriya suka amince da danƙa ragamar shugabanci na riƙon ƙwarya a hannun mataimakin shugaba Jonathan Goodluck. A lokacin da take madalla da wannan ci gaba da aka samu a Nijeriya jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Nijeriya Alla sam barka" domin kuwa bayan sama da watanni biyu na fama da giɓin siyasa sakamakon rashin lafiyar shugaban ƙasa Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa, a yanzu ƙasar ta samu shugaban riƙon ƙwarya da aka naɗa a hukumance domin tafiyar da al'amuranta. Sai dai kuma babban ƙalubalen dake gaban Jonathan Goodluck a halin yanzu shi ne neman bakin zaren warware rikice-rikicen dake addabar Nigeriya, kama daga rikicin yankin Niger Delta zuwa ga binciken musabbabin tashe-tashen hankulan yankin tskiya-maso-arewacin Nijeriya da kuma bala'in nan na cin hanci dake wa mahukuntan ƙasar katutu."

Nigeria Goodluck Jonathan
Muƙadashin shugaban Nijeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Ita ma jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi akan wannan ci gaba a Nijeriya, inda tace shugaban riƙon ƙwaryan Nijeriya Jonathan Goodluck yayi alƙawarin garambawul daidai da shugaba Umaru Musa 'Yar Aduwa, inda ya ce muhimman abubuwan da zai ba wa fifiko a cikin watanni masu zuwa sun haɗa da ci gaba da afuwa ga 'yan tawayen Niger Delta da binciko masu laifin ta'asar garin Jos domin gurfanar da su gaban kuliya da kuma yaƙi da cin hanci. A dai halin yanzu ba abin da za a ce illa a sa ido a ga salon kamun ludayinsa a cikin watanni masu zuwa.

Mawallafi : Ahmed Tijani Lawal