1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka a wannan mako

Mohammad Nasiru AwalAugust 11, 2006

Rikicin yankin Darfur na yammacin Sudan na kara rincabewa.

https://p.dw.com/p/BvPi
´Yan gudun hijira a Darfur
´Yan gudun hijira a DarfurHoto: AP

Jama´a barkanku da warhaka. A yau zamu fara ne da wani dogon rahoto da jaridar TAZ ta rubuta mai taken yakin lardin Darfur ya dauki wani sabon salo. Jaridar ta ce yayin da shugaban daya daga cikin manyan kungiyoyin ´yan tawayen lardin mai fama da rikici ya kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya da gwamnati a birnin Khartoum sannan ya samu wani mukami a cikin gwamnati, sai gashi fada ya sake yin muni a Darfur. Jaridar ta ce da farko dai an hango wanzuwar zaman lafiya a lardin bayan da aka rantsad da Minni Minawi shugaban ´yan tawayen kungiyar SLA a matsayin mai bawa shugaba Omar al-Bashir shawara ta musamman a birnin Khartoum, a matsayin wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya. To amma yanzu ´ya´yan kungiyar sun juyawa Minawi baya, wanda haka ya haddasa wani sabon rikici a Darfur. Yanzu haka dai daukacin ´yan tawayen na SLA sun hade da ´yan tawayen Justice and Equality Movement inda suka kafa kawancen kungiyar ´yan tawaye ta NRF. A ranar litinin da ta gabata kungiyar ta NRF ta yi ikirarin harbo wani jirgin saman daukar kaya na dakarun gwamnati.

Ita ma jaridar FAZ ta yi tsokaci akan halin da ake ciki a Darfur, inda ta ce ba wata alamar cewa nadin Minawi zai yi wani tasiri wajen kwantar da kurar rikici a Darfur. Domin tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya fada ya kara yin muni tsakanin kungiyoyin ´yan tawaye a yankin. Kuma ake zargin bangaren Minawi da keta hakkin ´yan Adam, inda ma wasu mazauna yankin ke yiwa bangaren na sa lakabi da ´yan janjaweed na biyu. To sai dai kuma a daidai lokacin da ake ci-gaba da rikicin na Darfur, gwamnatocin Sudan da Chadi sun fara wani yunkuri na yin sulhu tsakaninsu. A ranar talata da ta gabata shugaban Chadi Idris Deby da takwaransa na Sudan Omar al-Bashir sun ba da sanarwar maido da huldar diplomasiya tsakanin kasashen su bayan wata ganawa da suka yi a birnin Ndjamena. A cikin wani rahoto da ta buga jaridar TAZ ta ce kasar Libya ce ta shirya wannan ganawa tsakanin shugabannin. A kuma halin da ake ciki shugaban Senegal Abdoulaye Wade ya gaiyaci Deby da Al-Bashir zuwa kasarsa don kammala wannan sulhu.

Yanzu kuma sai tarayyar Nijeriya, inda ake ci-gaba da yin garkuwa da ma´aikatan mai ´yan kasashen waje. A sharhin da ta rubuta jaridar Die Welt ta ce bayan an yi awon gaba da wani Bajamushe ma´aikacin kamfanin Bilfinger Berger a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir dake tarayyar Nijeriya, a makon jiya, a wannan makon ma an sace wasu baki ma´aikatan mai su 4 wadanda suka hada da ´yan kasar Norway da Ukraine. Jaridar ta ce duk da gagarumin shirin raya wannan yanki da gwamnatin Nijeriya ta dauki alkawarin yi har yanzu sojojin sa kai na yankin na sace ma´aikatan mai don neman a biya su diyya. Ita kuwa jaridar TAZ labari ta buga game da sace wasu ma´aikatan mai guda biyu da suka hada da dan kasar Belgium da dan kasar Marokko, jiya a yankin na Nijer Delta. Jaridar ta ce yanzu yawan baki da aka yi garkuwa da su a kudancin Nijeriya sun kai mutum 10.

Yanzu kuma sai kasar JDK inda sakamakon farko da hukumar zaben kasar ta bayar ya yi nuni da cewa shugaba Joseph Kabila ke kan gaba da kashi 47 cikin 100 na kuri´un da aka kidaya yayin da tsohon madugun ´yan tawaye Jean-Pierre Bemba ke matsayi na biyu da kashi 24 cikin 100 sannan babu daya daga cikin sauran ´yan takara 22 daga cikin 33 da ya samu ko da kashi daya cikin 100. A rahoton da ta buga jaridar BAZ ta ce wannan sakamakon dai ya shafi kashi daya cikin 10 ne na mazabun kasar baki daya. Jaridar ta ce har in an ci-gaba da haka to shugaba Kabila zai lashe zaben ba tare da an gudanar da zagaye na biyu na zaben a ranar 29 ga watan okotoba ba. To jama´a karshen sharhunan jaridun Jamus din kenan akan nahiyar mu ta Afirka a wannan mako.