1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus

Lawal, TijaniFebruary 26, 2008

Ra'ayoyin jaridun Jamus kan lamuran Afurka

https://p.dw.com/p/DDp8
George W Bush da Laura Bush a Afrika.Hoto: AP

Kenya/Nigeria/Tchad/South Afrika

Da farko dai zamu fara ne da ra'ayin da jaridun Jamus suka bayar dangane da ziyarar da shugaban Amurka George W. Bush ya kammala a nahiyar Afurka. Misali a cikin nata sharhin jaridar Die Tageszeitung tayi batu ne a game da rabon nauyin aiki na fadar mulki ta White House a Afurka, inda take cewa:

Bisa ga dukkan alamu shugaba George W. Bush ba ya sha'awar jin labarai marasa dadi da matsaloli na Afurka a ziyarar da ya kai ga nahiyar a saboda haka ya dora wa sakatariyarsa ta harkokin waje Condoleeza Rice wannan alhaki na kai ziyara Nairobin Kenya domin nuna goyan baya ga kokarin sasantawa da tsofon sakataren MDD Kofi Annan ke yi a rikicin kasar da ya biyo bayan zabenta na watan desamban shekarar da ta wuce."

Nigeria

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Shugaba Bush ya kauce wa yankin Niger Delta a ziyararsa da ya kai ga kasashen Afurka duk kuwa da cewar kungiyar MEND ta wannan yanki ta gabatar da roko ga kasar Amurka da ta sa baki don kawo karshen rikicin yankin mai dimaim arzikin man fetur, wanda ita kanta Amurkan ke cin gajiyarsa. To sai dai kuma ko da yake ba wanda ya san irin martanin da Amurka zata mayar akan wannan roko, amma a daya bangaren bata ba da cikakken goyan baya ga gwamnatin dake mulki a Nijeriya saboda nuna kin amincewar da tayi da shawarar kafa wani sansanin sojan ko-ta-kwana na Amurka a harabar Nijeriya."


To ko hakan na da nasaba da canza shawarar da Amurkan tayi game da kafa sansanonin sojan nata na Africom a nahiyar Afurka. Ga dai abin da jaridar Süddeutsche Zeitung ke cewa:


"Ba zato ba tsammani Amurka ta canza shawararta game da kafa shelkwatar sojojinta na Africom a harabar wata kasa ta Afurka, bayan da da farkon fari ta bayyana niyyar yin hakan. A dai halin da ake ciki yanzun wasu ofisoshin sojan ne za a kafa domin tuntubar mahukunta na kasashen da lamarin ya shafa da kuma musayar ra'ayoyi da su. Amma fa a hakikanin gaskiya, babu wata kasa ta Afurka da tayi marhabin lale da kafa sansanin sojan Amurkan a harabarta, inda shugaban Nijeriya Umaru Musa 'Yar Aduwa ya fito fili ya bayyana wa Amurkan cewar tutur ba zai amince da hakan ba."


Nigeriya ta dauri niyyar zama kashin bayan zama daya daga cikin kasashe masu kakkarfan tattalin arziki tsakanin kasashe masu arzikin man fetur, kamar yadda jaridar Financial Times Deutschland ta nunar, sannan sai ta ce amma fa Nijeriya tana da wata matsala daya. Domin kuwa duk da dimbim arzikin mai da Allah Ya fuwace mata akasarin al'umar kasar na fama da talauci, inda aka ce kashi 52% daga cikinsu ma 'yan rabbana ka wadatamu ne dake zama hannu baka-hannu-kwarya. Sai dai abin madalla shi ne kasancewar sabuwar gwamnatin shugaba 'Yar Aduwa ta ankara da wannan matsala a sakamakon haka ta shiga ba da fifiko ga bunkasa tattalin arzikin kasar. To sai dai kuma masu tababa na nuna cewar, wannan ba shi ne karo na farko ba, an sha yi wa 'yan Nijeriya gafara sa, amma ba sa ganin ko kaho."

Tchad

Ita kuwa jaridar Stiftung Wissenschaft und Politik ta sake lekawa ne kasar Chadi, inda ta nuna tababarta a game da tasirin ayyukan rundunar kiyaye zaman lafiya na kasashen Turai EUFOR a takaice. Jaridsar ta ce:


"Fitowa fili da kasar Faransa tayi tana mai nuna son kai ga wani bangare a rikicin kasar ta Chadi ya sanya aka fara saka ayar tambaya a game da ainifin makasudin tura rundunar ta EUFOR zuwa wannan kasa, kuma hakan zai yi mummunan tasiri akan matakai na soja da KTT zata dauka a nahiyar Afurka nan gaba, saboda kasashen nahiyar zasu zura na mujiya suna masu bin diddigin ci gaban da za a samu a kasar ta Chadi."


Kasar Afurka ta Kudu na fama da matsalar karancin wutar lantarki, lamarin dake barazana, ba ma ga tattalin arzikinta na cikin gida ba, kazalika da janyewar 'yan kasuwa na ketare a kasar. A lokacin da take nazarin wannan matsala jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:


Ba dade ba da al'umar ATK ke wa takwarorinsu na Zimbabwe ba'a, inda suke cewar: Me Zimbabwe ke da shi, kafin a gabatar da kendir a kasar? Amma fa a halin yanzu murna ta fara komawa ciki, domin kasar da ta zama kashin bayan tattalin arzikin Afurka a zamanin baya take kuma shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya nan da shekaru biyu masu zuwa tana fama da matsalar karancin wuta, lamarin dake mummunan tasiri akan tattalin arzikinta da kuma harkokin sufuri a kasar."