1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaru akan Afirka

July 8, 2009

Afirka a Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/Ijf8
Zauren taron shugabannin Afirka a LibyaHoto: AP


A wannan makon jaridun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa dangane da al'amuran Afirka tare da ba da la'akari da taron ƙolin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Afurka a ƙasar Libiya. Jaridar Die Tageszeitung tayi amfani da wannan dama domin bitar ire-iren matsaloli da muzantawar da 'yan gudun hijira na Afurka ke fuskanta a hannun mahukuntan ƙasar ta Libiya, wadda shugabanta Mu'ammar Ghaddafi ke fafutukar neman tabbatar da haɗin kan Afurka ƙarƙashin wata gwamnati ta tsakiya. Jaridar ta ce:


"Ƙasashen Turai dai, a halin da ake ciki yanzun, sun dogara ne kan ƙasashen arewacin Afurka don hana tuttuɗowar 'yan gudun hijira zuwa Turai. A yayinda Aljeriya ake hukunta baƙin haure, ita Libiya sansanoni masu kama da na gwale-gwale ta kafa a cikin hamada, inda mahukuntanta kan tsare 'yan gudun hijirar domin mayar da su ƙasashensu. Tuni ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan-Adam kamarsu Amnesty International da Pro Asyl ke Allah Waddai da waɗannan sansanoni da ƙasashen Turai suka taimaka wa Libiya, mai karɓar baƙoncin taron ƙolin ƙungiyar tarayyar Afurka, wajen gina su, musamman ma dangane da irin muzantawa da take haƙƙin ɗan Adam da mahukunta Libiya ke yi wa 'yan gudun hijirar a waɗannan sansanoni."

Soldaten in Mogadishu, Somalia
MogadishuHoto: AP


Ita kuwa jaridar Rheinischer Merkur madalla tayi da abin da ta kira cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da zaman haƙuri da juna da ake yi tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar Ghana, wanda ta ce abu ne da ka iya zama abin koyi ga ƙasashe da dama na nahiyar Afurka. Jaridar ta ce:

Ghana Fußball Africa Cup Stadion in Accra Ghana gegen Nigeria
GhanaHoto: AP


"Wannan zama na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka tsakanin Musulmi da Kiristoci a Ghana tuni ya ɗauki wani tsayayyen fasali a hukumance, inda a shekara ta 1994 aka kafa wani kwamitin haɗin guiwa don tuntuɓar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci 'yan Katolika. Kwamitin ta kan tura wakilanta don ziyarar makarantu da haɗa kan jama'as da ɗinke duk wata ɓaraka da ka taso. Tuni ma kwamitin mai mazauninsa a garin Tamale na arewacin Ghana mai rinjayen Musulmi ya buɗe wata tasha ta rediyo tare da taimakon ofishin jakadancin Jamus a Ghana, bisa wannan manufa."


Al'amura sai ƙara taɓarɓarewa suke yi a ƙasar Somaliya sakamakon ba ta kashin dake ci gaba da wanzuwa tsakanin sassan da basu ga maciji da juna a rikitacciyar ƙasar dake gabacin Afurka. Jaridar Neues Deutschland tayi bayani akan haka tana mai cewar:


"Babban abin da ake tsoro a game da waɗannan tashe-tashen hankula shi ne ka da a wayi gari ƙasar ta zama wani dandalin yaɗa aƙidar jihadi ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar al-Qa'ida, lamarin da ba shakka zai ta da zaune tsaye a duk faɗin yankin gabacin Afurka."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed