1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariár Saddam Hussaini a Iraqi

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOw

A ranar Laraban nan mai zuwa ce zaá fara shariár tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussaini, daga cikin laifukan da ake tuhumar Saddam da aikatawa sun hada da kisan gillar da aka yiwa wasu kurdawa su kimanin 5000 da iskar gas mai guba a kauyen Halabja a cikin watan Maris na shekarar 1998, da kuma yakin da ya gwabza da kasar Iran wanda ya kwashe tsawon shekaru takwas inda mutane kimanin miliyayan daya suka hallaka kana da mamayar kasar Kuwaiti a shekarar 1990. Sauran laifukan sun hada da zargin kisan mutane 143 mabiya darikar Shia dake zaune a kauyen Dujail a matakin daukar fansa na yunkurin hallaka shi da aka yi.Saddam wanda zai baiyana tare da wasu manyan mukarraban sa uku da kuma manyan jamíyar Baath su hudu na iya fuskantar hukuncin kisa. A cikin watan Disambar shekara ta 2003 sojojin Amurka suka kama Saddam bayan tsegunta musu wurin da ya buya. Tun daga lokacin da aka kama Saddam din da kuma matakan kafa mulkin dimokradiyya a kasar, har yanzu basu haifar da da mai idanu ba. A waje guda dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama na tababa a game da ko alkalan kotun zasu iya gudanar da shariár bisa gaskiya da adalci.