1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariár Saddam Hussaini

September 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuiL

A yau Litinin ake cigaba da shariár tsohon shugaban ƙasar Iraqi Saddam Hussaini, sai dai kuma lauyoyin dake kare shi sun ce zasu ƙauracewa zaman shariár. Babban lauyan Saddam ɗin yace sun ɗauki matakin ne domin nuna ɓacin ran su ga hura wutar da gwamnatin ke yiwa kotun wadda ke tuhumar Saddam a kan laifukan kisan kiyashi. A makon da ya gabata, gwamnatin Iraqin ta kori babban Alƙalin kotun Abdullah al Ameri bayan da yace Saddam bai yi mulkin kama karya ba. Naɗin sabon Alkali Mohammed al-Oreibi ya sanya lauyoyin Saddam ficewa daga Kotun. Hakazalika, Alkalin ya umarci Saddam da ya fita daga kotun bayan da ya ƙalubalance shi. Saddam da muƙarraban sa su shida na fuskantar tuhumar kisan ƙare dangi bisa jagorantar farmakin soji a kan ƙabilar Kurdawa a tsakanin shekarun 1987 zuwa 1988. Masu gabatar da ƙara sun ce mutane fiye da 180,000 ne aka kashe a yayin wannan farmakin.