1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

040808 Zuma Prozess

Govender, Subry Pietermaritzburg DW Englisch August 5, 2008

An Gurfanar da shugaban jam´iyar ANC Jacob Zuma gaban ƙulliya.

https://p.dw.com/p/Eqc1
Jacob Zuma gaban ƙuliyaHoto: AP



Shugaban Jam´iyar ta ANC Jacob Zuma na daga sahun wanda jama´a ke kyautata zaton zai gaji shugaba Tabon Mbeki a karagar mulkin Afrika ta Kudu.

To saidai har yanzu ya na fama da matsaloli ta fannin sharia´ a sakamakon zargin da ake yi masa da hannu a cikin al´ammuran cin hanci da karbara rashawa, na dalla dubu 560 da ya karɓa.

A game da haka a jiya ya gurfana gaban ƙulliya, to saidai kotu ta saurare shi a yayin da dubunan magoya bayansa ke shirya wani ƙasaitatcen taron gangami, kusa da kotu don nuna goya bayan ga Jacob Zuma.

Wannan dubunan jama´a sun taro a kotun birnin Pietermaritzburg, inda su kayi ta rera kalamomin cewar makirci da zagon ƙasa ba zai hana Jacob Zuma ba ya zama shugaban ƙasar Afrika ta Kudu  a shekara mai zuwa.

Shugaban matasan jam´iyar ANC Julius Malema, na daga wanda suka jagoranci wannan zanga zanga, ya kuma yi ƙarin bayyani kamar haka:

Burinmu shine mu tabbatar da shi a matsayin shugaban ƙasa, a game da haka, za mu yi takalmi da duk wanda ya buƙaci dabaibaiye wannan aniya.

A cikin kotun lauyoyin Jacob Zuma, sun yi kira ga alƙalai suyi sharia´a ta adalaci, kamar yadda tayi a sharia´ar watan Satumber na shekara da ta gabata, inda aka yi masa ƙagen lalata da ƙananan yara.

Sannan lauyoyin sun buƙaci kotu ta gurfanar da hukumar da tayi wa Zuma wannan ƙage da nufin ɓata masa suna.

A na sa ran kotu ta yanke hukunci a game da wannan sharia´anan gaba a yau.

To saidai a wani mataki mai kama da allura ta tono galma, shari´ar ta Jacob Zuma ta bankaɗo cewar shima shugaban Afrika ta Kudu Tabon Mbeki ya karɓi cin hanci na dalla miliyan kussan huɗu daga wani kamfanin ƙasar Jamus mai suna Man Ferrostaal, zargin da kakakinsa Mukoni Ratshinga ya musanta:wannan zargi ne da ba shi da tushe bare makama, sabbatu wanda ba ta kamata ma ba mutum ya kula da su.

Tuhumar da akewa Jacok Zuma da kuma shi kansa Tabon Mbeki, sun raunana jam´iyar ANC matuƙa, da dama daga magoya bayanta, na tare da baƙin ciki,  a game da yadda wannan jam´iya sannu a hankali ke kaucewa daga turba mai inganci da tsofan shugaban Nelson Mandela ya ɗora ta akai.