1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar birnin Nürnberg ta kasance tushen kafa kotun kasa da kasa

November 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvKD

Shugaban kotun kasa da kasa ta birnin The Hague Philippe Kirsch ya bayyana shari´ar birnin Nürnberg da aka yiwa tsofaffin jami´an gwamnatin ´yan NAZI da cewa wani abin tarihi ne na fannin shari´a. Lokacin da yake magana a birnin Nürnberg Kirsch ya ce fara wannan shari´a shekaru 60 da suka wuce ya zama kyakkyawan abin koyi ga MDD lokacin da ta amince da kafa kotun duniya a shekarar 1998. Kirsch yayi kira ga dukkan kasashen duniya da su amince da wannan kotu, domin ta haka ne kawai zata samu nasarar tafiyar da ayyukanta. A yau dai ne aka yi bukin cika shekaru 60 da fara shari´ar ta birnin Nürnberg, wadda aka yiwa tsofaffin jami´an gwamnatin ´yan NAZI. A wannan shari´a da aka yiwa shugabannin ´yan NAZI guda 22, a karon farko cikin tarihin duniya daulolin da suka yi nasara a yakin duniya na biyu su gurfanad da mutanen da aka zarga da aikata laifukan yaki da kisan kare dangi.