1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

261009 ICTY Karadzic

March 1, 2010

An cigaba da shari'ar tsohon jagoran Sabiyawan Bosniya Radovan Karadzic a kotun ƙasa da ƙasa dake The Hague dangane da tuhumar laifukan yaki

https://p.dw.com/p/MHDO
Tsohon jagoran Sabiyawan Bosniya Radovan KaradzicHoto: AP

Ana tuhumar tsohon jagoran Sabiyawan Bosnia Radovan Karadzic da aikata laifukan yaƙi da kuma kisan ƙare dangi a lokacin yaƙin Bosniya Herzegovina a shekarar 1992 zuwa 1995. Joji O-Gon Kwon wanda ya jagoranci zaman shari'ar ya sanar da cigaba da sauraron shari' ar tare da jin bahasi daga wanda ake ƙara wato Radovan Karadzic. Karadzic mai shekaru 64 da haihuwa na fuskantar tuhumar laifuka goma sha ɗaya waɗanda suka haɗa da kisan Koratiyawa da Musulmi su kimanin dubu ɗari ɗaya a lokacin yaƙin Bosniya a tsakanin shekarun 1992 zuwa 1995 wanda ya tagaiyara mutane fiye da miliyan biyu.

Tsohon Jagoran na Sabiyawan Bosniya ya faɗawa kotun cewa abin da ya aikata jihadi ne akan Musulman yankin, yana mai zargin masu shigar da ƙara na Majalisar Ɗinkin Duniya dake The Hague da gabatar da bayanan da ba na gaskiya ba waɗanda ya ce an yi amfani da su wajen tuhumarsa da laifin kisan ƙare dangi da cin zarafin bil Adama.

A wani jawabi da yayi a baya gabanin ɓarkewar yakin Karadzic yayi barazana ga Kroatiyawa da kuma Musluman Bosniya da suka yi yunƙurin ɓallewa daga Yugoslavia wanda Sabiyawa ke da rinjaye yana mai cewa.

"Ku yi tunani fa, ta haka zaku iya jefa Bosniya cikin mawuyacin hali. Kuma ku sani idan har yaƙi ya ɓalle to ku sani Musulmai da Koratiyawa ba za su iya kare kansu ba."

Ba da jimawa ba ne bayan wannan jawabi nasa yaƙi ya ɓalle a Bosniya wanda ke zama yaƙi mafi muni a nahiyar Turai tun bayan yaƙin duniya na biyu.

Ga abinda daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu daga cin zarafi da kuma keta haddin bil Adama a lokacin yakin na Bosnia Murat Tahirovic yake cewa.

"An yi min rauni a ƙirji da kuma ciki. A wannan lokaci wani ɗan sanda ya yi amfani da kulki ya riƙa cakawa a inda na ji rauni. An kuma yi min duka na kawo wuƙa da cin zarafin da bai misaltu ba. Kuma dukkan waɗannan ´yan sandan Sabiya sune suka riƙa yi mana."

Karadzic wanda ke kare kansa a gaban shari´ar an zarge shi da shirya maƙarƙashiyar kisan gilla ga Musulmai a Srebrenica yankin da a wancan lokaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana a matsayin tudun mun tsira. An yi ƙiyasin cewa sojojin Sabiya sun yiwa Musulmai maza da yara ƙanana su kimanin 8,000 kisan gilla.

Sai dai kuma Karadzic ya shaidawa zaman kotun cewa babu wani yunƙuri ko kaɗan na korar Musulmai ko kuma Koratiyawa daga yankin inda ya zargi Musulman da dagewa wajen neman ɓallewa daga yankin don kafa ´yantacciyar ƙasa tasu.

Ya kuma gabatar da takardu da hotunan bidiyo domin tabbatar da abinda ya kira hujja ta manufofinsa.

A cikin watan Augustan shekarar 2008 ne dai aka cafke Radovan Karadzic a birnin Belgrade bayan tsawon shekaru 13 yana ɓuya domin gujema hukunci.

Idan dai an tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa zai fuskanci hukuncin kisa.

Mawallafa: Filip Slavkovic/Abdullahi Tanko Bala

Edita: Mohammad Nasiru Awal