1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

September 16, 2009

A wannan makon aka yi shari'ar Lubna Hussein a ƙasar Sudan, wadda mahukuntan ƙasar suka zarge ta da saka wando, wanda suka ce wai ya saɓa da shari'ar musulunci.

https://p.dw.com/p/JiIb
Lubna Ahmad HusseinHoto: Lubna Ahmad Hussein

Wannan shari'ar dai ta ɗauki hankalin jaridun Jamus matuƙa da aniya. A cikin rahoton da ta bayar akan shari'ar jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

"'Yar jaridar nan ta ƙasar Sudan Lubna Hussein, wadda aka yanke mata hukunci sakamakon sanya wando, tana gwagwarmaya ne don neman haƙƙin mata a Sudan. Tuni dai aka canza hukuncin daga bulala 40 zuwa tarar kuɗi. Amma saboda kasancewar Lubna Hussein ta ce ba zata biya kuɗin ba za a tsare ta a kurkuku tsawon wata ɗaya. Ta yayata shari'ar a bainar jama'a ne saboda ta janyo hankalin mutane zuwa ga halin da mata ke ciki a ƙasar Sudan. Tun bayan gabatar da shari'ar musulunci a arewacin Sudan shekaru 20 da suka wuce a duk shekara sai an bulale dubban mata."

Kongo Soldaten in Kisangani
Sojojin Kongo a KisanganiHoto: AP

A wannan mako wata kotun soja a Kisangani dake gabacin Kongo ta yanke hukuncin kisa akan wasu Turawa 'yan ƙasar Norway su biyu bisa zarginsu da laifuka na kisa da leƙen asirin ƙasa. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ce ta ba da wannan rahoto, inda ta ci gaba da cewar:

"Ana zargin fursinonin biyu ne da bindige direban motarsu ta haya har lahira. Sai dai kuma sun musunta wannan zargi inda suka ce wasu 'yan bindiga ne suka kai farmaki kan motar tasu, inda suka kashe direban sannan su kuma suka samu kafar tserewa."

Har yau ana fama da cin hanci ha zalunci a dukkan ɓangarori na rayuwa a ƙasar Kongo a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda tayi bayani tana mai cewar:

"Wasu azzalumai ne ke tafiyar da harkar haƙar ma'adinai a ƙasar Kongo. A wani bincike da majalisar dattawa ta ƙasar ta gudanar an gano cewar akan yi sama da faɗi na kashi 80 cikin ɗari na ma'adinan da ake fitarwa zuwa ƙetare, musamman ma a ɓangaren ma'adanin zinariya."

Somalia islamistischer Miliz in Mogadischu Kämpfe
Mayaƙan rundunar ´yan kishin Islama a MogadishuHoto: AP

Gwamnati a Somaliya na iƙirarin shiga tattaunawa da masu zazzafan ra'ayin addini, kamar yadda jaridar Der Tagesspiegel ta rawaito. Jaridar ta ce:

"Akwai iƙirarin cewar a karon farko an shiga zauren tattaunawa tsakanin gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Somaliya da ƙungiyoyin musulmi dake adawa da ita. To sai dai kuma duk da haka dakarun ƙungiyoyin musulmin masu zazzafar aƙida na ci gaba da kai farmaki. A ɗaya ɓangaren kuma an ce sojojin Habasha sun sake kutsawa Somaliyar a 'yan makonnin da suka wuce. Kuma ƙungiyar Tarayyar Afurka ta ƙara wa'adin sojojinta na zaman lafiya a Somaliya."

Robert Mugabe Präsident Zimbabwe
Shugaba Robert Mugabe na ZimbabweHoto: AP

A cikin wata sabuwa kuma ƙasashen Afurka su nema da a soke takunkumin da aka ƙaƙaba wa Zimbabwe. A cikin rahotonta game da wannan ci gaba jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"A taronsu na Kinshasa ƙasashen gamayyar tattalin arziƙin kudancin Afurka sun yi kira ga ƙasashen yammaci da su soke takunkumin dake kan Zimbabwe ta la'akari da irin ci gaban da gwamnatin wucin gadi ta ƙasar ta cimma. To sai dai wannan bayanin ya saɓa da wanda jami'an diplomasiyyar yammaci suka bayar a game da yunƙurin da magoya bayan Mugabe ke yi na hana ruwa gudu bisa manufa. Ƙasashen na yammaci na fatan samun ƙarin matsin lamba akan Mugabe ƙarƙashin sabon shugaban Afurka ta Kudu Jacob Zuma."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal