1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar Saddam Hussain za ta fara a yau laraba

October 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvOo

Nan gaba a yau ne kotun mussaman da Amurikawa su ka girka a kasdar Iraki ke gurfanar da tsofan shugaban kasar Saddam Husain.

Mahimman leffikan da a kotun ta tuhumi tsofan shugaban da su,a shariar ta yau, sun shafi aikata kissan kiyyasau, ga wasu mutane 143, da kuma gana ukuba ga wasu karin iyalai 399 ,a garin Dujail da ke tazara kilomita 60, a arewancin Bagadaza.

Saddam zai bayyana gaban kotu tare da wasu mujtane 7 na hannun dammar sa.

A jajibirin wannan shari´a, mai dubun tarihi,daruruwan mutane magoya bayan Saddam Hussain, a mahaifar sa, da ke Tikrit, da wasu sauran garuruwa sun shirya tafiyar jerin gwano, domin jaddada goyan bayan su, ga tsofan dan mulkin kama karyar.

Rahotani na nuni da cewa, akwai alamun kotu ta yanke hukunci kissa, ga Saddam Hussain da sauran mutanen 7;

Saidai kungiyar kare hakkokin bani Adama, ta Amnisty International, ta nuna adawa da hukuncin kissa.

Lauyan Saddam Hussain, ya ce zai bukataci a daga shari´ar ta yau, har zuwa watani 3 masu zuwa.

A bangaren hare hare kuwa, yan yakin sunkuru, sun bingige mataimakin gwamnan jihar Anbar, tare da sojin tsaran lafiyar sa.

Sannan wani sojin Amurika daya, ya bakunci lahira a yammacin jiya.