1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariar Saddam Hussein

Hauwa Abubakar AjejeApril 5, 2006

A yau tsohon shugaban kasar Iraqi Saddam Hussein ya fara amsa tambayoyi a kotu,karo na farko tun fara shariar tasa.

https://p.dw.com/p/Bu0p
Hoto: AP

A jiya ne dai kotu ta sanarda cewa Saddam zai fuskanci wasu sabbin zargi,na kisan kiyashi akan Qurdawa a karshen 1980.

Saddam din ya fara amsa tambayoyi game da laifukan nasa inda kuma yaki amincewa ya sanya hannu kan wasu takardu,yana mai fadin cewa,sai halartacciyar kotu ta kasa da kasa ce kadai zata iya nuna adalaci a shariar tasa.

Ya kuma yi Allah wadai da maaiaktar harkokin cikin gida ta Iraqin,inda yace ita ke da alhakin kashe dubban yan Iraqi,yana mai zargin alkalin kotun da tsoron ministan harkokin cikin gida na yanzu,wanda tuni yan sunni suke zarginsa da laifin haddasa tashe tashen hankula na dariku a kasar.

A yau din dai Saddam shi kadai ya baiyana gaban kotun,yana mai dora ayar tambaya kan halalcin kotun,yace,ya kamata kuma yan Iraqi su tashi tsaye game da mamayar dakarun Amurka a kasarsu.

A game da zargi da kotu takeyiwa Saddam da mukarrabansa guda 7 na kisan mutane 148 yan shia a garin Dujail,bayan yunkurin kashe shi da sukayi,Saddam yace ya dauki mataki bisa tsarin dokar kasar a wancan lokaci.

Hakazalika an zarge shi da laifin kashe Qurdawa kusan 100,000,tare da lalata kauyukansu a lokacin wani bore na Anfal.

Saddam ya shiga musayar yawu da alkalin wanda wasu ke ganin ba zai yi adalci saboda ya fito ne daga Halabja inda ake zargi saddam ya kashe mutane 5,000,da iska gas mai guba a 1988.

Saddam ya ja da takardu da aka fitar dauke da sanya hannunsa na kisan kiyashi da akayi,yana mai cewa,zai dauki alhakin dukkan laifi da aka dora masa muddin dai an tabbatar hannu da aka sanya kan wadannan takardu nasa ne,inda yace ya tabbata cewa,takardun na jabu ne.

A halin da ake ciki a kasar ta Iraqi,a yau din akalla mutane 3 sun rasa rayukansu wasu 5 suka samu rauni,cikin wani harin bam da aka kai a birnin bagadaza,mintuna kadan bayan wani bam din ya raunata wasu mutane 13.

A garin Basra dake kudancin Iraqin kuma,an harbe wani farfarfesa har lahira,a kofar makarantar da yake koyarwa.

Rundunar sojin Amurka kuma ta sanarda cewa sojin da yan sanda na Iraqi sun kwato wasu farar hula 3 da ake garkuwa da su a Mosul.

A wata sanarwar ta dabam kuma,sojin Amurkan sunce sun kai hari kan wata maboyar yan taadda,a Yusufiya inda suka tsare mutane 9 daya kuma ya rasa ransa,yayinda da dama kuma suka tsere.

Suka ce sun gano makamai da dama a wannan yankin na Yusufiyya,inda a makon daya gabata,aka harbo wani jirgi mai saukar angulu na Amurka wanda yayi sanadiyar rayukan matukan jirgin 2.