1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Shugabannin 'yan tawayen Kongo a The Hague

November 24, 2009

A zaman farko na shari'ar da ake wa Katanga da Chui a kotun ƙasa da ƙasa dake garin The Hague dukkansu biyu sun ce ba su da laifi

https://p.dw.com/p/KeD0
Madugun 'yan tawaye Germain Katanga a zauren kotun ƙasa da ƙasa ta The HagueHoto: AP

A yau talata ɗin nan ne aka fara zaman shari'ar wasu shuagabannin 'yan tawaye na ƙasar Kongo su biyu a kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka na yaƙi dake garin The Hague na ƙasar Holland. Ana zargin shuagabannin 'yan tawayen guda biyu, Germaine Katanga mai shekaru 31 da Mathieu Ngudjolo Chui dake da shekaru 39 na haifuwa da laifin kisan ƙare dangi akan mazauna wani ƙauye a ƙasar Kongo a shekara ta 2003

Germain Katanga, wanda dakarunsa ke masa taken Simba yana ɗan shekaru 24 da haifuwa ne lokacin da ya ba wa dakarunsa umarnin aiwatar da kisan ƙare dangin akan mutane kimanin dubu takwas da kuma wasu sama da miliyan ɗaya da aka fatattakesu daga gidajensu sakamakon saɓani na ƙabilanci. Rahotanni sun ce tsofon janar Katanga, wanda a yanzu yake da shekaru 31 na haifuwa, a matsayinsa na kwamandan dakarun FRPI ta ƙabilar Ngiti ya ba da haɗin kai ga kwamandan dakarun ƙabilar Lendu ta FNI Ngudjolo Chui don aiwatar da wannan ɗanyyen aiki a ƙauyxen Bogoro dake lardin Ituri a gabacin Kongo. Dukkansu biyu ana zarginsu da tilasta yara ƙanana da ba su cika shekaru 15 da haifuwa ba aikata wannan ta'asa. Kotun da ƙasa da ƙasa dake garin The Hague ta daɗe tana mai tunani kafin ta tsayar da shawarar gurfanar da maduguwannin 'yan tawayen biyu, lokaci guda, a gaban kuliya. A lokacin da yake bayani game da shawarar da kotun ta tsayar farfesa Christoph Safferling daga jami'ar Marburg kuma darektan cibiyar bincike da tara bayanai akan miyagun laifuka na yaƙi cewa yayi:

"Ta la'akari da neman tantance gaskiya shawarar cin shari'ar bai ɗaya abin madalla ne. Amma kuma a lokaci guda akwai wata matsala da zata iya kunno kai, saboda ba za a samu sauƙin tafiyar da shari'ar ba. Musamman ma idan aka yi la'akari da cikakkiyar damar da waɗanda aka yi wa laifin ke da ita wajen ba da shaida a kotun ta ƙasa da ƙasa. Mai yiwuwa hakan ya haifar da tafiyar hawaniya ga shari'ar, kamar dai yadda aka saba gani a zamanin baya."

A dai zaman farko da aka yi dukkansu biyu sun musunta laifin da ake zarginsu da aikatawa na kisan ƙare dangi akan 'yan ƙabilar Hema dake yankin arewa-maso-gabacin lardin Ituri na janhuriyar demoƙaraɗiyyar Kongo. Shi dai Germain Katanga yayi nuni da cewar tun bayan taso ƙeyarsa da aka yi zuwa garin The Hague shekaru biyu da suka wuce ya bayyana cewar ba shi da wani laifi, kuma har yau yana kan bakansa na cewar bai aikata laifi ba. Shi ma dai abokin tafiyarsa Ngudjolo Chui ya bi sau a irin wannan iƙirari. Tun kuwa da farko fari kotun ta ƙasa da ƙasa tayi watsi da laifin fyaɗe da ake zargin madugwannin 'yan tawayen guda biyu da aikatawa, lamarin da ya haifar da raɗaɗi mai tsananin gaske a zukatan waɗanda ta'asar ta shafa da danginsu. Wannan manufa ka iya yin tasirin akan shari'ar da ake wa ɗan kisan ƙare dangin Serbiya Radovan Karadzic. Domin ita masa tasa shari'ar tana fama da tafiyar hawaniya sakamakon rashin cikakkun bayanai akan laifukan da ake zarginsa da aikatawa. To sai dai kuma farfesa Christoph Safferling yayi bayani da cewar:

"Dangane da Katanga da Chui, ba zai ta'azzara akan mai ɗaukaka ƙara a kotun ta ƙasa da ƙasa wajen gabatar da wasu tabbatattun laifuka ba, bisa saɓanin yadda lamarin yake dangane da Karadzic".

Su dai dangin waɗanda ta'asar ta rutsa dasu a ƙauyen Bogoro dake gabacin Kongo ba abin da suke sauraro illa ganin an kamanta adalci wajen hukunta Katanga da Chui akan laifukan da suka aikata.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu