1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Somaliyawa

May 25, 2010

An fara shari'ar mutanen da ake zargi da laifin yin fashi a tekun Somaliya

https://p.dw.com/p/NWfl
'Yan fashin tekun SomaliyaHoto: AP

A birnin Rotterdam mai tashar jiragen ruwa a ƙasar Netherlands, an fara zaman shari'a dake zama irinta ta farko a nahiyar Turai, ga wasu 'yan ƙasar Somaliya su biyar da ake zargi da fashin jirgin ruwa. A cikin watan Janairun bara, sojojin ruwan ƙasar Denmark suka cafke mutanen a Tekun Somaliya, lokacin da suka yi ƙoƙarin farma wani jirgin ɗaukar kaya na Netherlands, sannan makwanni huɗu baya aka tisa ƙeyarsu zuwa ƙasar ta Netherlands. Idan aka tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa, ana iya yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru 12 a gidan kurkuku. To sai dai masu kare su na nuna shakku ga sahihancin shari'ar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi