1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar 'yan tawayen Sudan

June 16, 2010

Agobe za'a fara shari'ar 'yan tawayen Sudan, a kotun hukunta masu aikata man'yan laifuka ta duniya.

https://p.dw.com/p/NsCs

Shugabannin 'yan tawayen Sudan biyu, sun isa birnin Hague bayan da suka miƙa kansu don bayyana a gaban kotun hukunta masu aikata man'yan laifuka ta duniya.  Kotun ta bayyana cewa Abdullah Banda Abbakar da kuma Saleh Muhammed Jerbo Jamus, za su gurfana gaban alƙali a gobe, inda kuma daga baya za su ci gaba da kasancewa a cikin ƙasar ta Holland har izuwa wani lokaci. Mutanen biyu an zargesu da aikata laifin yaƙi, lokacin da suka kai hari a wani sansanin sojoji dake Darfur a shekara ta 2007, inda suka jagoranci mayaƙa kimanin dubu ɗaya, waɗanda suka aukawa ruddunar kiyaye zaman lafiya ta tarayyar Afirka, kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga sojojin da raunata wasu da dama.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu