1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharon yace zai ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da Palsdinawa

December 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvEy

Jamiyar Kadima ta Prime ministan Israila, Ariel sharon,ta baiyana a yau din nan cewa,ta yanke shawarar mayar da tattunawar zaman lafiya da Palasdinawa,ya zama daya daga cikin batutuwa mafiyai muhimmanci a gabanta.

Kuriar jin raayin jamaa da aka gudanar kwanan nan,ta nuna cewa akwai alamun cewa sabuwar jamiyar da Sharon ya kafa a watan da ya gabata,zata lashe zaben watan maris mai zuwa.

Wata jaridar kasar mai suna Maariv a yau tace,Sharon ya fice daga jamiyar Likud don ya samu damar ci gaba da tataunawar zaman lafiya da Palasdinawa ba tare da tsangwama ba.

A cewar jaridar ,Jamiyar Kadima tayi imanin cewa ci gaba da tattaunawa da palasdinawa itace kadai hanya da zata samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin,tace kuma zata taimaka wajen tabbatar da kafa kasar palasdinu mai yancin cin gashin kanta.