1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar goge sunan Sudan daga Ƙasashe 'Yan Ta'adda

November 12, 2010

Gwamnatin Amirka ta yi alƙawarin fitar da Sudan daga jerin ƙasashe masu ba wa ta'addanci goyan baya idan gwamnati ta girmama sakamakon ƙuri'ar raba gardama

https://p.dw.com/p/Q7UF
Iyalin Bongo na daga cikin shuagabannin da ake zarginsu da wawason dukiyaHoto: AP

A yau dai zamu fara ne da wani sabon ci gaban da aka samu dangane da shuagabannin Afirka dake wawason dukiya suna jigilarsu zuwa bankunan ƙasashen Turai, inda mahukunta a Faransa suka fara ɗaukar matakai na bincike domin ɗaukaka ƙara gaban kotu. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Kawo yanzun dai masu fafutukar kare haƙƙin ɗan-Adam da yaƙi da cin hanci sun sha fama da wahala wajen gabatar da ƙara kan shuagabanni masu wawason dukiyar ƙasashe suna kaiwa ƙetare, ta yadda za a sake mayar da wannan dukiya zuwan ƙasashen da lamarin ya shafa. Amma a yanzu sun cimma wata nasara ta farko, inda babbar kotun Faransa ta tsayar da shawarar ba wa ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta Transparency International damar ba da shaida akan iyalan wasu shuagabannin Afirka guda uku da ake zarginsu da laifin wawason dukiyar ƙasa. Wannan kuwa wani babban ci gaba ne da ba a taɓa ganin shigensa a fafutukar yaƙin da matsalar cin hanci ba."

Ita kuwa mujallar GIGA Focus Afrika hangen yiwuwar kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Paul Biya 'yar shekara 28 a ƙasar Kamaru. Mujallar ta ce:

Präsident Paul Biya, Kamerun
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: AP Photo

"Ko da yake a sakamakon kwaskwarimar da aka yi wa daftarin tsarin mulkin Kamaru shekaru biyu da suka wuce, shugaba Paul Biya dake mulki tun daga shekara ta 1982, na da ikon sake tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa a shekara mai kamawa ta 2011, amma fa tun misalin shekaru ashirin da suka wuce ne gwamnatinsa ta yi asarar wata ƙwaƙƙwarar madogara a game da halascin mulkinta. Bisa saɓanin sauran ƙasashen Afirka, ita Kamaru, iskar canjin demoƙraɗiyyar da ta kaɗa a farkon shekarun 1990 bata yi tasiri akanta ba. Kuma a fafutukar tabbatar da akalar mulki a hannunsa Paul Biya ya sanya jam'iyyarsa ta tilasta aiwatar da garambawul ga daftarin tsarin mulkin ƙasar dake ƙayyade wa'adin mulki a Kamaru."

Amirka ta yi wa Sudan alƙawarin goge sunanta daga jerin ƙasashen da ake zarginsu da ɗaure wa ta'addanci gindi idan har fadar mulki ta Khartoum zata amince da sakamakon ƙuri'ar raba gardama da za a gudanar watan janairu mai zuwa a game da 'yancin kan kudancin Sudan, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito. Jaridar ta ci gaba da cewar:

Sudan Wahlen Kandidat Salva Kiir
Salva Kiir na kudancin SudanHoto: AP

"Yunƙurin na Amirka dai shi ne na baya-baya nan a cikin jerin matakan da ta sha ɗauka a ƙoƙarin shawo kan fadar mulki ta Khartoum ta daina tunani gabatar da wani sabon yaƙi a kudancin Sudan. A tsakanin jami'an diplomasiyyar ƙasashen Turai ma dai akwai masu ba da shawarar dakatar da umarnin cafke shugaba Umar Al-Bashir har tsawon shekara guda. Idan har shugaban na Sudan ya fito fili ya amince da sakamakon ƙuri'ar raba gardamar ana iya soke umarnin ma kwata-kwata."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu