1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shawarar kasashe hudu game da kwamitin sulhu

May 19, 2005

Kasashen Jamus da Japan da Indiya da Brazil sun gabatar da wata takardar shawara a game da garambawul ga kwamitin sulhun MDD

https://p.dw.com/p/Bvbp
ministocin harkokin wajen Jamus, Brazil, Japan da Indiya
ministocin harkokin wajen Jamus, Brazil, Japan da Indiya

A daidai lokacin da shugaban kwamitin kula da manufofin ketare na majalisar dokokin Jamus Volker Rühe yak ai ziyara ma’aikatar harkokin wajen Amurka dake birnin Washington domin bin bahasi akan irin goyan baya da Jamus zata iya samu a kokarinta na neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na MDD, jaridar Washington Post ta fasa kwai, inda ta ambaci sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tana mai nuna adawar ba wa Jamus irin wannan kujera ta dindindin a kwamitin sulhu bayan ganawar da tayi da wasu gaggan jami’an siyasar kasar ta Amurka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Richard Boucher, a diplomasiyyance ya nuna cewar kasa daya kwal da Amurka take ba wa goyan baya dangane da garambawul ga kwamitin sulhu na MDD ita ce kasar Japan. Bai fito fili ya karfafa ko kuma akalla ya musunta rahoton jaridar ta Washington Post ba, a game da kos hin a hakika sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice na kyamar karbar Jamus a wannan kwamiti na ‚yan gata da suka hada da Amurka da Rasha da China da Faransa da kuma Birtaniya. Ita dai Washington Post ta ambaci Condoleeza Rice tana mai fadin cewar ita kam bata ga wani dalilin da zai sanya a karbi karin wata kasa ta nahiyar Turai a kwamitin sulhu na MDD ba. Bugu da kari kuma ita kanta Kungiyar Tarayyar Turai tana bin manufofin ketare bai daya ne tsakanin kasashenta. An dai saurara daga kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkan Richard Boucher yana mai bayanin cewar:

2. O-Ton Boucher:

„Die Tatsache, dass…

Goyan bayan da muke ba wa kasar Japan baya ma’anar cewa muna ba da goyan baya ga wani bangare na shawarwarin garambawul da aka gabatar. Zamu yi bitar dukkan shawarwarin daki-daki, abin da ya hada har da shawarar baya-bayan nan ta wadanda aka kira wai gungun kasashe hudu.

A farkon wannan makon ne kasashen Jamus da Brazil da Indiya da kuma Japan suka ba da shawarar karbar dawwamammun wakilai guda shida da kuma wasu hudu da zasu rika karba-karba a tsakaninsu a kwamitin sulhun na MDD. Shi kuwa Boucher, abin da yake nufi da bayanin nasa shi ne, ba lalle ba ne kasar Amurka ta ba wa Jamus goyan baya, saboda kawai tana ba wa kasar Japan goyan baya.

Tun watanni da dama da suka wuce ne kasar Amurka ta ki ta fito fili ta yi batu a game da bukatar Jamus ta samun dawwamammiyar kujera a kwaitin sulhu, hatta ita kanta sakatariyar harkokin waje Condoleeza Rice ba ta fito fili ta ce uffan ba a lokacin da ta kawo ziyara Berlin kwanan baya. A baya ga kasar Amurka ita ma China tana tababa a game da muhimmancin karbar Jamus a kwamitin na sulhu in har an tsayar da shawarar karbar karin kasashe na dindindin a wannan muhimmiyar kafa ta MDD.