1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarar tura sojan Jamus zuwa Kongo

May 18, 2006

Aikin kiyaye zaman lafiya na KTT a Kongo na nuna irin canjin da aka samu ga manufofin kungiyar dangane da Afurka

https://p.dw.com/p/Btzz

Wani abin da aka lura da shi a ‘yan makonnin da suka wuce dai shi ne kusan ba wani jami’in siyasar Jamus dake sha’awar ganin an tura sojojin kasar zuwa Kongo. Amma a jiya laraba sai ga shi majalisar ministoci da tsayar da shawarar shigar da sojoji kusan 800 a matakin na tsaron zaman lafiya a janhuriyar demokradiyyar Kongo dake can kuryar tsakiyar Afurka. Ga alamu kuwa wannan shawarar an tsayar da ita ne sakamakon matsin lamba daga sauran kawayen Jamus a Kungiyar Tarayyar Turai. Ya zama tilas Kungiyar ta Tarayyar Turai ta dauki wannan mataki saboda MDD ta kasa tabuka wani abin a zo a gani. Domin kuwa da abu mafi alheri da rafusa shi ne a bunkasa yawan sojojin kiyaye zaman lafiya na MDDr dake kasar Kongo daga dakaru dubu 17 zuwa dakaru dubu 20. Amma sau biyu ana gabatar da shawarar haka a kwamitin sulhu kuma Amurka na hawa kujerar na ki. A sakamakon haka ake nemi KTT da ta cike wannan gibi. Kungiyar zata tura dakarun soja 1500 domin ba da kariya ga masu sa ido akan hada-hadar zaben na kasar Kongo da jami’an diplomasiyya da tabbatar da tsaron filayen jiragen sama da kuma kai taimako ga sojojin MDD in har sun fuskanci barazana. Maganar dai dake akwai shi ne kasancewar wannan mataki an gabatar da shi ne don nuna halin sanin ya kamata kawai saboda sojoji 1500 ba zasu iya tabbatar da tsaron wata kasa da fadinta ya kai yammmacin Turai baki dayanta ba. Kazalika murna tana iya komawa ciki a game da wannan mataki idan al’amura sun rikide suka dauki wani sabon salo a cikin kiftawa da Bisimillah ta la’akari da zaman dardar da ake ci gaba da fama da shi a kasar ta Kongo. A sakamakon haka ne ma aka sha fama da tafiyar hawainiya dangane da shawarar gwamnatin Jamus a game da shigar da sojojin kasar a wannan mataki mai kasada. Hakan ya taimaka aka bata lokaci wajen yi wa matakin wani takamaiman shirin da ya dace. Musamman ma ta yadda sojojin zasu kasance a cikin shirin ko ta kwana ko da wata sabuwa ka taso. Amma duk da haka tura sojojin yana da muhimmanci matuka ainun, kuma dukkan al’umar kasar ta Kongo na madalla da haka saboda yadda suke Allah-Allah su ga kasar ta su ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan rikici na tsawon shekara da shekaru. Kazalika tura sojojin tamkar wata alama ce dake yin nuni da irin canjin da aka samu ga manufofin KTT dangane da nahiyar Afurka. Domin kuwa kungiyar ta ci alwashin taimaka wa nahiyar a kokarinta na yaki da matsaloli irinsu yunwa da talauci da cututtuka da kuma yake-yake na basasa.