1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin Karbar Turkiyya A Kungiyar Tarayyar Turai

September 7, 2004

Bisa ga ra'ayin kantoman KTT akan karbar karin kasashe Günter Verheugen kasar Turkiyya ta samu ci gaba matuka ainun ta yadda za a iya tsayar da wani takamaiman wa'adi na fara shawarwari da ita

https://p.dw.com/p/Bvgi

A cikin ‚yan makonni kalilan masu zuwa ne hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) zata kaddamar da rahotonta a game da irin ci gaban da Turkiyya take samu bisa manufa. Wannan rahoton shi ne zai zama ginshikin shawarar da shuagabannin kasashen kungiyar zasu tsayar dangane da shiga shawarwarin karbar kasar ta Turkiyya. Da wuya ne dai za a cimma wani takamaiman kuduri sai dai kawai a yi fatan cewar duk wata shawarar da za a tsayar zata samu ne a cikin basira. Ita dai gwamnatin Turkiyya da cika da yawa daga cikin sharuddan da aka shimfida mata kuma a saboda haka ya zama wajibi a duba al’amuranta tsakani da Allah. Domin kuwa ko da yake kasar na samun goyan baya daga kantoman KTT a game da karbar karin kasashe Günter Verheugen da gwamnatin Jamus da kuma wasu tsaffin jami’an siyasar kasashen kungiyar, amma fa masu adawa da manufar karbarta a kungiyar suna nan akan bakarsu. A hakika dai muhimmin abin da ake bukata shi ne Turkiyyar ta cika sharuddan kudurin Copenhagen, wanda shi ne ainifin mizanin da aka shimfida na karbar karin kasashe a inuwar Kungiyar ta Tarayyar Turai, kafin a karbeta a kungiyar watan-wata rana. Wadannan sharudda kuwa sun hada da sahihin tsarin mulkin demokradiyya da daidaituwar tattalin arziki kasa da girmama hakkin tsiraru, kamar yadda aka bukata daga sabbin kasashen tsakiya da na gabacin Turai da aka karbesu a kungiyar baya-bayan nan. Wadannan su ne ainihin sharuddan kuma duk wani abin da zai biyo baya kari ne kawai aka kirkiro. Amma ainifin dalilin adawar karbar kasar ta Turkiyya shi ne kasancewar akasarin al’umarta Musulmi ne. Alal-hakika har yau da sauran rina a kaba kafin Turkiyya ta kai matsayin da ake bukata domin zama cikakkiyar wakiliya a gamayyar ta kasashen Turai, amma abin lura shi ne tun shekaru aru-aru da suka wuce ne ke bakin kokarinta wajen bin manufofin kasashen yammacin Turai duk da matsaloli na cikin gida da ta sha fama da su, kuma ta la’akari da haka kasar ta cancanci da a yi hulda da ita tsakani da Allah ko da kuwa zai dauki wani lokaci ne mai tsawo nan gaba kafin a karbeta a kungiyar ta tarayyar Turai. Wani abin mamaki a nan shi ne yadda a bangare guda aka ba wa kasar Turkiyyar damar zama cikakkiyar wakiliya a kungiyar tsaro ta NATO, amma a daya bangaren ake fama da cece ku ce a game da karbarta a KTT. Akwai masu korafi a game da dimbim kudin da za a kashe wajen karbar Turkiyya a kungiyar suna masu fatali da ainifin gudummawar da zata bayar ko zata iya bayarwa a nata bangaren. Domin kuwa a baya ga taimakawar da zata yi wajen fadada al’amuran cinikin kasashen Turai, kazalika zata zama wata babbar gada mai sadarwa tsakanin kasashen da na Musulmi, musamman a daidai wannan zamanin da ake fama da wasu daidaikun ‚yan ta’adda dake amfani da sunan addini domin cimma bukatunsu na siyasa da yada angizo.