1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin sulhunta takaddamar nukiliyar Iran

November 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvJ7

Kasashen Birtaniya, Faransa da kuma Jamus sun amince su koma kan teburin shawarwari da kasar Iran akan shirin ta na nukiliya da ake takaddama a kai. Da farko kamfanin dillancin labarun gwamnatin Iran wato IRNA ya rawaito cewar jakadun kasashen kungiyar EU 3 sun mika wata wasika wadda a ciki suka amince da sake komawa kan teburin shawarwarin a cikin watan desamba. To amma wani jami´in kungiyar EU ya ce kasashen Turan sun amince ne su gudanar da tattaunawa da nufin samun wata madogara ta komawa kan teburin shawarwarin a hukumance. Da farko kuwa kasashen 3 sun ce za´a koma ga shawarwarin ne a hukumance idan Iran ta daina sarrafa sinadarin uranium.